Dangote, Adenuga, Otedola da sauran manyan masu kudin kasar nan a yau

Dangote, Adenuga, Otedola da sauran manyan masu kudin kasar nan a yau

Masu kudi sun girgiza ko a ce su na kan girgiza a Najeriya da sauran kasashen Duniya saboda annobar COVID-19. A daidai wannan lokaci kuma a lokacin kasuwar wasu ta bude.

Mun kawo maku jerin manyan attjiran Najeriya a daidai wannan lokaci:

1. Aliko Dangote

Aliko Dangote wanda ya ba fam Dala biliyan $9.9 ya zarce kowa kudi a Nahiyar Afrika da Najeriya. ‘Dan kasuwar shi ne bakin attajirin da ya fi kowa kudi a Duniya

2. Mike Adenuga

Mike Adenuga shi ne na biyu a cikin attajiran Najeriya a 2020. Adenuga ne mai kamfanin Globacom, kuma ya yi fice a Afrika, Attajirin ya mallaki kimanin Dala biliyan 7.

3. Femi Otedola

Mista Femi Otedola shi ne shugaban kamfanin man Forte Oil wanda gidajen man su ya zagaye ko ina a Najeriya. Ana hasashen Otedola ya tada kai da abin da ya kusa Dala biliyan 2.

4. Jimoh Ibrahim

Wani babban mai kudi a Najeriya shi ne shugaban kamfanin Global Fleet Group wanda su ka yi fice a harkar mai, gidaje da inshora. Jimoh Ibrahim ya ba Dala biliyan 1 baya.

KU KARANTA: Attajiran Najeriya da su ka fito daga Yankin Arewa

Dangote, Adenuga, Otedola da sauran manyan masu kudin kasar nan a yau
Mike Adenuga Hoto: Wikipedia
Asali: Twitter

5. Pascal Uzoma Dozie

Mista Pascal Uzoma Dozie shi ne mutumin da ya yi sanadiyyar kafa Diamond Bank. Haka zalika shi ne shugaban kamfanin MTN a Najeriya. Ya mallaki kusan Dala biliyan 1.

6. Folorunsho Alakija

Mace ta farko a jerin ita ce Folorunsho Alakija, kuma Attajira ta shida a fadin Najeriya. Alakija wanda ta ke da fiye da dala biliyan 1 a Duniya ta na harkar mai da madaba’a.

7. Orji Uzor Kalu

Sanata Orji babban mai kudi ne wanda ya ke da kusan Dala biliyan 1. Ana rade-radin cewa tsohon gwamnan kasar ya karye kwanaki bayan farashin mai ya yi kasa a Duniya.

8. Jim James Ovia

Jim Ovia fitaccen mai kudi ne, ba don kawai ya ajiye Dala miliyan $900 ba. Dattijon mai shekaru 68 shi ne wanda ya kafa Zenith Bank shekaru 30 da su ka wuce.

9. Bola Shagaya

Bola Shagaya mai shekara 60 ta na cikin attajiran matan Afrika. Attajirar ta fito ne daga garin Ilorin, kuma ana jitar-jitar cewa abin da ta mallaka ya kai Dala miliyan 900.

10. Fifi Ekanem

Wata mace da ta samu shiga cikin wannan sahu ita ce Fifi Ekanem wanda a sanadiyyar harkar mai da kasuwancin kayan gine-gine ta tara abin da ya haura Dala miliyan 850.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel