Manyan jami’an yan sanda sun fara kamun kafa domin maye gurbin Ibrahim Magu a EFCC
- Manyan jami’an yan sanda sun fara kamun kafa don maye gurbin dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu
- An tattaro cewa manyan jami’an yan sanda da dama sun fara nuna ra’ayinsu na son zama shugaban EFCC na gaba
- Sai dai kuma, an ce jami’ai da ke kusa da shugaban kasar na so a ba wanda ba dan sanda ba mukamin shugabancin hukumar
Biyo bayan dakatar da Ibrahim Magu a matsayin mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), an tattaro cewa manyan jami’an yan sanda sun fara zawarci don maye gurbinsa.
A cewar jaridar The Leadership, manyan jami’an yan sanda da dama na kamun kafa domin zama shugaban EFCC na gaba.
Koda dai ba a ambaci sunan kowa ba a matsayin madadin Magu, an tattaro cewa jami’ai na kusa da shugaban kasa na neman kada a ba dan sanda mukamin shugabancin EFCC na gaba.
Wata babbar majiya ta fada wa jaridar cewa jami’an da ke son aikin sun fara kamun kafa a wajen mutanen da ke gwamnati domin ganin sun samu mukamin.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kama wasu manyan matsafa da ke kashe bayin Allah a Ibadan
“Jami’an yan sanda wadanda suke ganin sun cancanci aikin sun fara zantawa da manyan mutane a gwamnati domin ganin sun samu aikin. Amma shugaban kasar bai damu da batun wanda zai ci gaba daga inda Magu ya tsaya ba a yanzu,” in ji majiyar.
A gefe guda, mun ji cewa Dino Melaye, tsohon dan majalisa ya yi ba’a ga Ibrahim Magu, shugaban hukumar EFCC biyo bayan dakatar da shi da Shugaba Buhari ya yi.
Shugaban kasar ya shata wa Magu layi a ranar Talata, 7 ga watan Yuli, ta hanyar dakatar da shi sa’o’i 24 bayan hukumar tsaro na farin kaya (DSS) ta gayyace shi da kuma tsare shi.
Da yake martani ga lamarin Magu, tsohon dan majalisar ya je shafinsa na Twitter domin yi wa shugaban hukumar yaki da rashawar ba’a.
Ya ce ya yi gargadi a kan Magu amma Shugaba Buhari bai sauraresa ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng