Yanzu Yanzu: An kama wasu manyan matsafa da ke kashe bayin Allah a Ibadan

Yanzu Yanzu: An kama wasu manyan matsafa da ke kashe bayin Allah a Ibadan

- Yan sandan jihar Oyo sun kama wasu da ake zargin matsafa ne kan yawan kashe-kashen bayin Allah da ake yi a yankin Akinyele, Ibadan

- Mista Fatai Owoseni, hadimin Gwamna Seyi Makinde ne ya bayyana hakan yayinda yake jawabi a wani taro a Akinyele a ranar Laraba

- Owoseni ya ce bada jimawa ba rundunar yan sandan jihar Oyo za ta gurfanar da masu laifin

Jami’an yan sanda sun kama wasu da ake zargin matsafa ne kan yawan kashe-kashen bayin Allah da ake yi a yankin Akinyele, Ibadan, jaridar The Nation ta ruwaito.

Hadimin Gwamna Seyi Makinde na musamman a kan tsaro, Mista Fatai Owoseni ne ya bayyana hakan yayinda yake jawabi a wani taro a Akinyele a ranar Laraba, 8 ga watan Yuli.

Gidan radiyo mai zaman kansa na JAMZ 100.1 FM ne ya shirya taron.

Yanzu Yanzu: An kama wasu manyan matsafa da ke kashe bayin Allah a Ibadan
Yanzu Yanzu: An kama wasu manyan matsafa da ke kashe bayin Allah a Ibadan Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Owoseni ya ce bada jimawa ba rundunar yan sandan jihar Oyo za ta gurfanar da masu laifin.

Ya ce: “Koda dai babu gari da ba a aikata laifi, ina iya baku tabbacin cewa a yanzu haka da nake magana an kama masu kashe-kashen bayin Allah a yankin Akinyele.

“A ranar Talata, An kama masu laifin kuma akwai yiwuwar Kwamishinan yan sanda zai gabatar da taron manema labarai a yau.

“Amma ina iya fada maku kai tsaye cewa mutumin da ke da alhakin aikata hakan ya kai yan sanda suka wajen matsafan kuma a yanzu haka suna tsare.”

Owoseni ya jadadda bukatar jama’a su zamo masu lura da lamarin tsaro, inda ya ce kowani mutum na da rawar takawa wajen tsare al’umma.

KU KARANTA KUMA: Ibrahim Magu: Dino Melaye ya yi martani a kan dakatar da shugaban EFCC da Buhari ya yi

An kashe mutane wasu mutane biyar ta yanayi mai ban al’ajabi a garin cikin watanni biyu da suka wuce.

Sun hada da wata ‘yar shekara 29 da ke sa ran haihuwa, daliban babban makaranta biyu da wani yaro karami.

A gefe guda, mun ji cewa yan sanda sun kama wani da ake zargin dan fashi ne mai shekara 30 mai suna Abubakar Namalika.

Namalika ya tona cewa yana daga cikin wadanda suka kashe wani likita, Okpara Enoch, wanda ke aiki a cibiyar kiwon lafiya ta tarraya da ke Gusau, jihar Zamfara.

Ya ce ya samu N5,000 tukwicin kan kashe mutane bakwai da ya yi ciki harda marigayi Dr. Opara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel