A tsare Ibrahim Magu kamar yadda ya ce ayi mani da ina Gwamna – Fayose

A tsare Ibrahim Magu kamar yadda ya ce ayi mani da ina Gwamna – Fayose

- Tsohon Gwamnan Ekiti ya tofa albarkacin bakinsa game da abin da ke faruwa a EFCC

- Shi ma Dino Melaye ya yi magana bayan Shugaban kasa ya dakatar da Ibrahim Magu

- Tsohon Sanatan Kaduna, Shehu Sani ya yi irin habaicin da ya saba a shafinsa na Twitter

Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti ya yi magana a game da dakatar da mukaddashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu da aka yi daga aiki a ranar Litinin.

Tsohon gwamnan ya yi kira ga jami’an tsaro a Najeriya su sa idanu a kan tsohon shugaban na EFCC saboda ka da ya tsere daga kasar.

Ayo Fayose ya yi amfani da shafinsa na Twitter ya na bada shawara ga jami’an asiri na DSS, da ‘yan sanda da sojojin sama, su sa idanu a kan Ibrahim Magu wanda yanzu ake bincike.

Fayose ya ambaci jami’an hukumar kwastam masu yaki da fasa-kauri da jami’an kula da shige da fice su yi kokarin tirke jami’in kamar yadda ya yi masa a lokacin da ya ke gwamna a Ekiti.

“Kamar yadda Magu ya bada umarni a lura da ni duk da lokacin ina da garkuwa a matsayin gwamna mai-ci, shi ma dole a sa masa idanu, domin ka da ya tsere.”

KU KARANTA: Magu: Sai da na gargadi Buhari a baya - Dino Melayex

“EFCC, DSS, kwastam, ‘Yan sanda, jami’an lura da shiga da fice, ga aiki gare ku. Abin da mutum ya shuka, shi zai girba.” Inji Fayose.

Shi kuma Sanata Dino Melaye ya yi amfani da shafinsa na Twitter ya na mai cewa dama can ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari a game da sharrin Ibrahim Magu.

A cewar tsohon ‘dan majalisar a wani bidiyo, yanzu halin shugaban na EFCC sun fara bayyana gaban shugaban kasa Buhari bayan ya yi kunnen-kashi a lokacin da ake ba shi shawara.

Shi kuma Shehu Sani cewa ya yi: "A lokacin da farar kura ta ke farautar barewa, ta manta cewa damisa ta na bin ta a baya.”

Tsohon Sanatan na Kaduna ya bayyana wannan ne a kafar yada labarai na zamani, ya na shagube ga tsohon shugaban na EFCC wanda yanzu ake bincikensa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel