Buhari ya fara laluben wanda zai maye gurbin Magu
Fadar shugaban kasa ta fita cefanen wanda zai maye gurbin Ibrahim, mukaddashin shugaban hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arziki ta'annati da aka dakatar.
Hakan ya biyo bayan dakatarwar da fadar shugaban kasar ta yi masa kamar yadda wata majiya mai karfi daga fadar wadda ta bukaci a sakaya sunanta ta tabbatar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an gabatar wa da fadar shugaban kasar sunayen mutum hudu da kowannensu ya cancanci maye gurbin kujerar jagoranci a hukumar EFCC.
Sunayen mutane hudu da aka gabatar sun hadar da wani tsohon DIG; mataimakin sufeto janar na 'yan sanda DIG da kuma wani tsohon AIG; mataimakin sufeton janar na 'yan sanda.
Sauran biyun kuma wasu kwamishinonin 'yan sanda ne biyu wanda har a yanzu su na kan makamar su ta aiki.
Tun a ranar Litinin ne Magu ya bayyana a gaban kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa domin bincike kan zargin da ake yi masa na karkatar da akalar wasu kudade ta hanyar da ba su dace ba.
Kwamitin wanda Tsohon alkalin kotun daukaka kara, Mai Shari'a Ayo Salami yake jagoranta, ya gayyaci Magu domin ya wanke kansa daga laifukan da ake zargin ya aikata yayin jagoranci a hukumar ta EFCC.
Ana iya tuna cewa, a watan Yunin da ya gabata ne Ministan Shari'a Abubakar Malami, ya aikewa da shugaba Muhammadu Buhari wasikar kar ta kwana kan mukaddashin shugaban Hukumar EFCC wato Magu.
Legit.ng ta ruwaito cewa, Malami ya bukaci shugaban kasa Buhari ya tsige shugaban hukumar hana almundahanan daga mukaminsa bisa wasu zarge-zargen rashawa da akalla sun haura 20.
Daga cikin laifukan da Ministan ya ke zargin Magu ya aikata sun hadar da karkatar da akalar dukiyar da aka kwato daga hannun wadanda suka yi sama da fadin kudaden gwamnati.
Haka kuma Ministan yana tuhumar Magu da rashin yi masa biyayya duk da Hukumar EFCC tana karkashin Ma'aikatarsa ta Shari'a.
A cikin wasikarsa, Ministan ya ba da sunayen mutane uku da za su iya maye gurbin Ibrahim Magu, mukaddashin Shugaban Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki ta'annati, EFCC.
Malami wanda kuma shi ne Lauyan Koli na Najeriya, ya ba wa shugaban kasar shawara a kan mutane uku da zai iya zaba wajen maye kujerar Ibrahim Magu.
KARANTA KUMA: Kasashe 5 mafi karfi a nahiyar Afrika
Sunayen mutum uku da Ministan ya aikewa da Buhari su cikin wata wasika sun hadar da Mataimakin Sufeto Janar na 'Yan sanda, DIG Muhammad Sani Usman mai ritaya.
Sauran biyun su ne; Kwamishinan 'Yan sanda na Abuja, Bala Ciroma wanda shi ne shugaban kula da sashen gudanarwa na EFCC, da kuma wani Tsohon Mataimakin Sufeton 'Yan Sanda AIG daga jihar Kebbi.
Gabanin yanzu, Malami ya taba neman Buhari ya maye gurbin Magu da DIG Usman ko kuma Ms Diseye Nsirim-Poweigba, wata tsohuwar kwamishinan 'yan sanda a jihar Neja.
Ministan ya ba da shawarar a zabi daya daga cikin mutane biyun yayin da tsohuwar majalisar dattawa ta ki amincewa da nadin Magu a matsayin shugaban Hukumar ta EFCC.
Sai dai wata majiya kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito ta bayyana cewa, a yanzu shugaba Buhari bai da ra'ayin daukar Ms Diseye a matsayin wadda za ta gaji kujerar Magu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng