Shugaban ma'aikatan jihar Kwara, Alhaji Adisa, ya rasu

Shugaban ma'aikatan jihar Kwara, Alhaji Adisa, ya rasu

- Shugaban ma’aikatan jihar Kwara, Alhaji Adisa Logun, ya rasu yana da shekaru 73 a duniya

- Babban hadimi na musamman ga gwamnan jihar Kwana kan harkokin labarai, Fafoluyi Olayinka ne ya tabbatar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafin twitter

- An nada marigayi Aminu Adisa Logun a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Kwara a 2019, yan makonni kadan bayan rantsar da Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq

Allah ya yi wa shugaban ma’aikatan jihar Kwara, Alhaji Adisa Logun, rasuwa.

Babban hadimi na musamman ga gwamnan jihar Kwana kan harkokin labarai, Fafoluyi Olayinka ne ya tabbatar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafin twitter.

Ya rasu yana da shekaru 73 a duniya, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Shukakken Bam ya tashi da motar Sojoji, yayi sanadiyar mutuwar hafsan Soja, Abdullahi Alhassan

Shugaban ma'aikatan jihar Kwara, Alhaji Adisa, ya rasu
Shugaban ma'aikatan jihar Kwara, Alhaji Adisa, ya rasu Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ya ce: “Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Kwara, Aminu Adisa Logun, ya rasu. Shakka babu mutuwa itace abu na gaba bayan haihuwa. Bakar Talata ta zo a Kwara.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ngige ya bayar da hakuri a kan furucin Keyamo game da ayyuka 774,000

An nada marigayi Aminu Adisa Logun a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Kwara a 2019, yan makonni kadan bayan rantsar da Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq.

A wani labarin mun ji cewa tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na arewa maso yamma, Alhaji Inuwa Abdulkadir, ya rasu.

Koda dai babu wata tabbataciyar sanarwa daga mahukunta kan ko annobar korona ce ta kashe shi, wata majiya a Sokoto ta bayyana cewa ya rasu a ranar Litinin.

“Kwarai ya yi fama da rashin lafiya kuma ya rasu a safiyar yau,” in ji majiyar.

A wani labarin kuma, mun ji wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace diyar wani jigon APC, Alhaji Gimba Salihu Bako, a yankin Chiji da ke Abaji.

Alhaji Gimba, wanda dan takarar kujerar shugaban karamar hukumar Abaji ne ya tabbatar da sace diyarsa mai suna Hasiya Gimba da aka yi ga jaridar Daily Trust.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng