Da duminsa: Majalisa ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamnan Ondo

Da duminsa: Majalisa ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamnan Ondo

'Yan majalisar dokokin jihar Ondo sun mika bukatar tsige mataimakin gwamnan jihar, Agboola Ajayi.

'Yan majalisar na zargin Ajayi da matukar rashin da'a, jaridar The Punch ta ruwaito.

Ya bar jam'iyyar APC ma mulki zuwa jam'iyyar adawa ta PDP amma ya ki sauka daga kujerarsa.

An gano cewa 'yan majalisa 14 ne suke goyon bayan tsige Ajayi.

Har ila yau, an saka tsauraran matakan tsaro a gidan gwamnatin jihar a yayin da 'yan majalisar ke taro.

Amma domin gujewa tsige mataimakin gwamnan, Ajayi ya garzaya gaban wata kotun tarayya da ke Abuja inda ya bukaci kotun da ta hana majalisar tsigesa.

Ajayi yace ya yanke hukuncin mika bukatarsa gaban kotu don hana majalisar kokarin tsigesa daga kujerarsa bayan barin jam'iyyar APC da yayi zuwa ta PDP.

Da duminsa: Majalisa ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamnan Ondo
Da duminsa: Majalisa ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamnan Ondo Hoto: The Punch
Asali: UGC

A ranar Litinin, lauyan mataimakin gwamnan, I. Olatoke ya shigar da kara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda suke bukatar dakatar da yunkurin tsigesa tare da jaddada hakkinsa na 'yancin mu'amala.

Idan za a tuna, Agboola ta bakin hadiminsa Allen Sowore, ya zargi shirin tsigesa da ake yi. Ya ce gwamnan ya bai wa 'yan majalisa 19 daga cikin 23 N10 miliyan don su goyi bayan tsigesa.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da diyar jigon APC a Abuja

Sauran wadanda ya maka a gaban kotun sun hada da sifeta janar din 'yan sandan najeriya, kwamishinan 'yan sanda, hukumar jami'an tsaro ta farin kaya da kakakin majalisar jihar, David Oleyeloogun.

A halin da ci ciki, 'Yan majalisa tara na jihar Ondo sun tsame hannunsu daga yunkurin tsige mataimakin gwamnan.

A wani labari na daban, mun ji cewa jam'iyyar APC ta tsara yadda za ta dawo da zaman lafiya a tsakanin 'ya'yanta don samun damar lashe zabukan jihohin Edo da Ondo da ke karatowa.

Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya ce jam'iyyar za ta hanzarta sasanta 'ya'yanta a duk fadin kasar nan don dawo da zaman lafiya tare da lumana, jaridar The Nation ta ruwaito.

A ranar Litinin, 29 ga watan Yuni, jam'iyyar ta kafa kwamitin sasanci a babban ofishin jam'iyyar da ke Abuja.

Ta fidda tsari shida wanda za ta yi amfani da su wurin gyara zaman jam'iyyar a taron rantsarwar da aka yi wa 'yan kwamitin rikon kwaryar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel