'Yan bindiga sun yi garkuwa da diyar jigon APC a Abuja

'Yan bindiga sun yi garkuwa da diyar jigon APC a Abuja

- Masu garkuwa da mutane sun sace diyar wani jigon APC, Alhaji Gimba Salihu Bako, a yankin Chiji da ke Abaji

- Alhaji Gimba ya tabbatar da cewar ya samu kiran waya wurin karfe 2:30 na daren Litinin daga sirikinsa inda ya sanar da shi cewa an sace diyarsa

- Kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayyar, DSP Anjuguri Manzah, ya ce rundunar na bincike a kan garkuwar da aka yi da Hasiya kuma za a yi kokarin ceto ta

Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace diyar wani jigon APC, Alhaji Gimba Salihu Bako, a yankin Chiji da ke Abaji.

Alhaji Gimba, wanda dan takarar kujerar shugaban karamar hukumar Abaji ne ya tabbatar da sace diyarsa mai suna Hasiya Gimba da aka yi ga jaridar Daily Trust.

'Yan bindiga sun yi garkuwa da diyar jigon APC a Abuja
'Yan bindiga sun yi garkuwa da diyar jigon APC a Abuja Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Ya ce ya samu kiran waya wurin karfe 2:30 na daren Litinin daga sirikinsa inda ya sanar da shi cewa an sace diyarsa.

Ya ce 'yan bindigar sun kutsa gidan sirikinsa da ke kauyen Chiji mai nisan kilomita biyu daga garin Abaji inda suka yi awon gaba da Hasiya.

Kamar yadda yace, 'yan bindigar sun karbi kudi daga sirikinsa kafin su tafi duk da yace har yanzu dai basu tuntubesa ba.

KU KARANTA KUMA: Babu jihar da ta kai Kano samun yawan waraka daga cutar Korona

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayyar, DSP Anjuguri Manzah, ya ce rundunar na bincike a kan garkuwar da aka yi da Hasiya kuma za a yi kokarin ceto ta.

A wani labari makamancin wannan mun ji cewa wani rahoto daga kauyen 'yar Gamji na karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina ya bayyana, wasu 'yan bindiga 200 dauke da miyagun makamai sun kai hari tare da kashe mutane sama da 15.

'Yan bindigar da suka tsinkayi kauyen a kan babura, sun halaka manoman da suka samu a gona.

'Yan bindigar sun isa kauyen wurin karfe 10 na safe kuma sun yi ruwan wuta na a kalla sa'a daya, mazauna yankin suka sanar da Daily Trust.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel