Abin da ya sa na ajiye aiki a Gwamnatin Akeredolu – inji Ifedayo Abegunde

Abin da ya sa na ajiye aiki a Gwamnatin Akeredolu – inji Ifedayo Abegunde

- Ifedayo Abegunde ya bayyana dalilinsa na yin murabus daga gwamnatin Ondo

- Tsohon sakataren gwamnatin ya ce tun farko APC ba ta ci zaben 2016 ba

- Ya ce an yi amfani da wasu manya wajen dora Rotimi Akredolu a kan mulki

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Ondo, Ifedayo Abegunde, wanda ‘yan siyasa su ka fi sani da Abena, ya ce ya yi da-na-sanin aiki da gwamna Rotimi Akeredolu.

Ifedayo Abegunde wanda ya bar kujerar SSG ta sakataren gwamnatin jiha a makon nan ya fito ya bayyana abin da ya sa yayi murabus daga gwamnatin APC.

Abegunde ya ce ba a yi masa adalci a tafiyar mai girma gwamna Rotimi Akeredolu, don haka ya tattara ina sa-ina sa, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP mai adawa.

‘Dan siyasar ya bayyana haka ne a lokacin da aka yi hira da shi a wani gidan rediyo da ke garin Akure, jihar Ondo a jiya ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, 2020.

A wannan hira, Abegunde ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ce ta lashe a zaben 2016 a jihar Ondo, amma a karshe aka bada sanarwar Rotimi Akeredolu ya zama sabon gwamna.

A cewar Ifedayo Abegunde, an yi amfani da karfin mulki a jihar Ondo da wajen jihar, wajen bankara hukumar INEC domin ta bankara zaben domin APC ta yi nasara a 2016.

KU KARANTA: An alakanta Jagororin PDP da ‘dan damfarar da aka kama a kasar waje

Abin da ya sa na ajiye aiki a Gwamnatin Akeredolu – inji Ifedayo Abegunde
Ifedayo Abegunde
Asali: UGC

Ya ce: “Akeredolu ya fadi zabe, ya sha kasa a hannun ‘dan takarar PDP, Eyitayo Jegede, karfin mulki da wasu jiga-jigan APC aka yi amfani da su har INEC ta ce Akeredolu ya ci zabe.”

“Akeredolu bai lashe zaben 2016, mu mu ka yi yadda mu ka yi ya zama gwamna. Mu na da jiga-jigan cin zabe a bayanmu, ba za mu sake mara masa baya ba. Wannan karo zai sha kashi.” Inji sa.

Bayan shekaru uku da rabi ‘dan siyasar ya ce ba zai iya zama a cikin gwamnatin da ta jefa talakawan jihar Ondo cikin halin wahala ba, har ake tunawa da gwamnatin baya.

Mista Abegunde ya ce rikicinsa da gwamna a dalilin cin-kashin da ake yi masa ta sa ya hakura da aikinsa. Abegunde ya kuma karyata zargin cewa ana aikowa ofishinsa miliyan biyar duk wata.

A cewarsa, an kai lokacin da ba zai iya daukar dawainiyar magoya bayansa ba domin gwamnan ba ya sakin kudi domin ayi aiki a ofishinsa, wannan ya sa ya yi murabus, ya sauya-sheka.

Tsohon SSG din ya ce babu masu jin dadin gwamnatin APC mai-ci illa iyalin gwamna Akeredolu da na kusa da shi. Amma bai bada wasu hujjoji da za su gamsar da abin da ya ke fada ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel