Yanzu-yanzu: WAEC ta sanar da ranar fara jarrabawa

Yanzu-yanzu: WAEC ta sanar da ranar fara jarrabawa

- Hukumar jarrabawa ta WAEC ta sanar da ranar fara jarrabawar masu kammala sakandire na shekarar 2020

- Za a yi jarabawar tsakanin 4 ga watan Augusta zuwa 5 Satumban 2020

- Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajuiba ne ya sanar da hakan a yayin taron kwamitin yaki da cutar korona ta kasa

Hukumar jarrabawa ta yammacin Afrika (WAEC) ta sanar da ranar fara jarrabawar masu kammala sakandire na wannan shekarar.

Wannan sanarwar ta zo ne a yayin bayanin da kwamitin yaki da cutar korona ta fadar shugaban kasa (PTF) karkashin shugabancin Boss Mustapha, ke yi a Abuja.

Yanzu-yanzu: WAEC ta sanar da ranar fara jarrabawa
Yanzu-yanzu: WAEC ta sanar da ranar fara jarrabawa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Kwamitin yaki da cutar korona ta kasa ya tabbatar da cewa za a yi jarabawar tsakanin 4 ga watan Augusta zuwa 5 Satumban 2020.

Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajuiba ne ya sanar da hakan a yayin taron.

Kamar yadda hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter: "Gwamnantin tarayya ta sanar da cewa za a fara jarabawar WAEC daga ranar 4 ga watan Augusta zuwa 5 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: DSS ta hana 'yan jarida shiga inda ake tuhumar Magu a Aso Villa

"Karamin ministan ilimi ne ya sanar da hakan a jawabin kullum na kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da korona a Abuja."

A gefe guda, mun ji a baya cewa gwamnatin jihar Kano ta yi magana dangane da jita-jitar da ke yaduwa a tsakanin al'umma na cewa a yau Litinin, 6 ga watan Yuli, za a bude makarantu ga wani rukuni na dalibai.

Legit.ng ta fahimci cewa, wasu daga cikin rukunin daliban da gwamnatin tarayya ta ba da umarnin a bude musu makarantu, sun shirya abinsu sun tafi makarantu da safiyar yau ta Litinin.

Sai dai fa sun riski makarantun a rufe, lamarin da ya sa a dole suka dawo gida ba bu shiri kuma ba tare da sun yi farin ciki a kan lamarin ba.

A yayin da 'yan kwanakin nan al'umma jihar Kano suka yi ta rade-radin za a bude makarantu a yau Litinin, wani gargadi da gwamnatin jihar ta yi ya disasashe duk wani tsammaninsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng