'Zamu dauki fansa': Buhari ya yi magana a kan harin da Boko Haram suka kaiwa jirgin UN

'Zamu dauki fansa': Buhari ya yi magana a kan harin da Boko Haram suka kaiwa jirgin UN

Wadanda suka kitsa kai wa jirgin majalisar dinkin duniya (UN) hari a daura da Damasak, a jihar Borno, zasu 'dandana kudarsu' kamar yadda shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ci alwashi.

Sugaban kasa ya ce gwamnati za ta dauki fansar harin da aka kai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da suka hada da karamin yaro mai shekara biyar.

Ana alakanta kai harin da masu rajin yakin jihadi a yankin arewa maso gabas, musamman jihar Borno.

A ranar Juma'a ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa mayakan Boko Haram sun bude wa wani jirgi mai saukan ungulu mallakar Majalisar Dinkin Duniya (UNHAS) wuta a Damasak, a karamar hukumar Mobbar da ke arewacin jihar Borno.

Duk da haka, jirgin ya lallaba ya dawo sansaninsa a Maiduguri jim kadan bayan harin da aka kai masa a ranar Alhamis 2 ga watan Yulin 2020.

UNHAS na taimakawa ne wurin rabon abinci da karkashin shirin samar da abinci na duniya a yankin.

HumAngle ta ruwaito cewa an kai hari a jihar Borno, kwana guda bayan Gwamnan jihar, Babagana Zulum ya jagoranci wata tawaga zuwa Damasak don raba wa fiye da gidaje 12,000 tallafin abinci.

ISWAP ta amsa cewa ita ce ta kai harin na Damasak a tashan Amaq da ta saba amfani da shi wurin wallafa ayyukan ta tare da kira ga mutane su shiga su tallafa mata.

'Zamu dauki fansa': Buhari ya yi magana a kan harin da Boko Haram suka kaiwa jirgin UN
Jirgin UN
Asali: UGC

Majiyar Legit.ng ta gano cewar jirgin, UNHAS, da aka kai wa harin fari ne da tambarin UN a jikinsa kuma samfurin Bell 412 da 212 ne da aka tura yankin domin ayyukan jin kai.

DUBA WANNAN: Kamar a fim: Yadda jiragen yakin sojoji suka dinga ruwan wuta a wasu maboyar Boko Haram

A cikin wani jawabi da kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya fitar, shugaba Buhari ya bayyana harin a matsayin abin takaici tare da cin al washin cewa gwamnati za ta dauki fansa.

Shugaba Buhari ya bayyana harin a matsayin nuna tsoro da rauni a bangaren mayakan kungiyar Boko Haram.

Buhari ya bawa 'yan Najeriya da kasashen ketare tabbacin cewa gwamnatinsa zata kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Kazalika, shugaba Buhari ya bukaci dukkan kungiyoyi da hukumomin da ke aikin jin kai a yankin arewa maso gabas suke hada kai da kwamandan rundunar atisayen sojoji a duk lokacin da zasu je wani wuri daga Maiduguri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel