NCF za ta shawo kan matsalar shugabanci a Najeriya - Balarabe Musa

NCF za ta shawo kan matsalar shugabanci a Najeriya - Balarabe Musa

- Babban jigon arewa Balarabe Musa ya ce sabuwar kungiyar siyasa mai suna National Consultative Forum (NCF) da aka kafa za ta shawo kan matsalar shugabanci nagari a fadin kasar nan

- Musa ya ce ya amince da zama dan sabuwar kungiyar siyasar don ceto Najeriya daga matsanancin matsaloli da take fuskanta

- Ya jadadda cewa ba a yi wa Najeriya mulkin da ya dace kuma hakan ne yasa kasar ke bukatar ingantaccen shugabanci

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa, a ranar Lahadi ya ce sabuwar kungiyar siyasa mai suna National Consultative Forum da aka kafa za ta shawo kan matsalar shugabanci nagari a fadin kasar nan.

Musa ya kara da cewa, ya aminta da zama dan sabuwar kungiyar siyasar don ceto Najeriya daga matsanancin matsaloli da take fuskanta.

Idan za mu tuna, NCF ta sanar da kafuwarta ta bakin Abubakar Umar, wanda tsohon gwamna ne a karkashin mulkin soja.

NCF za ta shawo kan matsalar shugabanci a Najeriya - Balarabe Musa
NCF za ta shawo kan matsalar shugabanci a Najeriya - Balarabe Musa Hoto: The Punch
Asali: Depositphotos

Amma kuma tsohon gwamna kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa, Olisa Agbakoba da Femi Falana sun nesanta kansu daga sabuwar kungiyar siyasar.

Musa tare da sauran 'yan kungiyar, sun sanar da cewa ba a yi wa Najeriya mulkin da ya dace kuma hakan ne yasa kasar ke bukatar ingantaccen shugabanci, jaridar The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Goyon bayan Obaseki: Aliko Dangote ya yi karin bayani

A wani labari na daban, mun ji cewa a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya caccaki dattawan arewa inda ya zargesu da mayar da yankin baya a maimakon tabbatar da ci gabanta.

Da yake magana a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin gidauniyar tunawa da Ahmadu Bello karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, Bello ya ce shugabannin yankin da suka zo bayan Ahmadu Bello sun ki dorawa daga inda ya tsaya.

Gwamna Bello ya zargi shugabannin da kunna wutar rikici na kabila da addinai wanda ya hana yankin zaman lafiya tare da kawo zubar jini.

Ya ce duk da yankin ta samar da manyan masu kudi, har yanzu yankin ne koma baya saboda yadda jama'ar suka ki saka hannun jari tare da shigewa gaba ta bangaren kawo ci gaba.

A don haka ya yi kira ga dattawan yankin da su yi koyi da hallayar Sardauna don ci gabanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel