Goyon bayan Obaseki: Aliko Dangote ya yi karin bayani

Goyon bayan Obaseki: Aliko Dangote ya yi karin bayani

- Mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya nesanta kansa daga batun goyon bayan tazarcen Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo

- Dangote ya ce a matsayinsa na babban dan kasuwa ya mayar da hankali ne wajen kawo ci gaba ta hanyar sanar da ayyukan yi ba wai siyasa ba

- Ya jadadda cewa hakan wani yunkuri ne na bata masa suna

Aliko Dangote, hamshakin mai kudin Afrika ya musanta batun goyon bayan Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo a karo na biyu da yake neman zarcewa.

Da yake magana ta hannun mai magana da yawunsa, Anthony Chiejina, Dangote ya bayyana rahoton cewa yana goyon bayan Obaseki a matsayin wani yunkuri na bata masa suna, jaridar The Cable ta ruwaito.

Ya ce a matsayinsa na shugaba a fagen kasuwanci, ya mayar da hankali wajen ci gaba, samar da ayyukan yi da kuma taimakon jama'a ba wai siyasa ba.

Goyon bayan Obaseki: Aliko Dangote ya yi karin bayani
Goyon bayan Obaseki: Aliko Dangote ya yi karin bayani Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Wannan ne karo na farko da na ga ana amfani da sunan ubangidana wurin yakin neman zabe kuma hakan ya zama dole in dakatar dasu don guje wa sake faruwar hakan a gaba," yace.

"Tattaunawa da aka ce an yi da Dangote a Abuja duk ta bogi ce, mai yunkurin dasa gaba da bata masa suna. Aliko Dangote bai fita daga jihar Legas ba tun daga ranar 19 ga watan Maris ta 2020. Kada a ja sunansa da mutuncinsa a cikin al'amarin yakin neman zabe na ko waye.

"Aliko Dangote dan kasuwa ne wanda ya mayar da hankali wurin ayyukan ci gaba, samar da aikin yi da kuma taimakon jama'a. Baya nuna goyon bayan kowa a jihar Edo ko wata jihar ta Najeriya."

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo a karkashin jam'iyyar PDP zai kara da Osagie Ize-Iyamu na jam'iyyar APC a zaben gwamnoni na ranar 19 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Shugaban APC na arewa maso yamma, Inuwa Abdulkadir, ya rasu

A wani labari na daban, mun ji cewa kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP, a ranar Juma'ar da ta gabata, ya nada gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna a jihar Edo.

Jam'iyyar ta sanar da hakan ne a kan shafinta na Twitter, inda ta bayyana gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, a matsayin mataimakin kwamitin yakin neman zaben.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel