Tsohon shugaban APC na arewa maso yamma, Inuwa Abdulkadir, ya rasu

Tsohon shugaban APC na arewa maso yamma, Inuwa Abdulkadir, ya rasu

- Allah ya yi wa tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na arewa maso yamma, Alhaji Inuwa Abdulkadir rasuwa

- Inuwa ya kuma kasance mamba a kwamitin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da aka rushe kwanan nan

- Wata majiya a Sokoto ta bayyana cewa jigon jam' iyyar mai mulki ya rasu ne a safiyar yau Litinin bayan ya yi fama da rashin lafiya

- Sai dai babu wata tabbataciyar sanarwa daga mahukunta kan ko annobar korona ce ta kashe shi

Wani tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na arewa maso yamma, kuma mamba a kwamitin masu ruwa da tsaki da aka rushe kwanan nan, Alhaji Inuwa Abdulkadir, ya rasu.

Koda dai babu wata tabbataciyar sanarwa daga mahukunta kan ko annobar korona ce ta kashe shi, wata majiya a Sokoto ta bayyana cewa ya rasu a ranar Litinin, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Shugaban APC a arewa maso yamma, Inuwa Abdulkadir, ya rasu
Shugaban APC a arewa maso yamma, Inuwa Abdulkadir, ya rasu Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Hawaye sun kwaranya yayinda manyan yan Najeriya 3 suka mutu sakamakon cutar a rana 1

“Kwarai ya yi fama da rashin lafiya kuma ya rasu a safiyar yau,” in ji majiyar.

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa an sha ‘yar dirama a ranar Lahadi a Oluyole, gidan marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, lokacin da aka hana mataimakin gwamnan jihar Rauf Olaniyan shiga wajen addu’an kwana takwas na rasuwarsa, wanda aka gudanar a harabar gidansa.

Iyalan marigayin sun sanar da cewar taron addu’an zai zama na takaitattun jama'a, inda suka bukaci jama’a da su kalla ta yanar gizo kamar a Zoom, YouTube da Facebook.

Olaniyan ya isa gidan da misalin 11:20 na safe a ayarin motoci biyar. Amma da ya kofar da zai shigar dashi hanyar gidan Ajimobi, sai yan sanda da sauran jamián tsaro suka dakatar da ayarin motocin.

Suka ce lallai sai dai motar mataimakin gwamnan ne kadai za a bari ya shiga unguwar don halartan taron.

Amma da suka isa gidan Ajimobi, sai suka kara tarar da kofar a rufe. Hadiman mataimakin gwamnan sun gabatar da ubangidansu amma aka sanar masu da cewar an rufe kofar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel