Gwamnoni 3 da wasu fitattun 'yan Najeriya 5 da suka kamu da korona a makon da ya gabata

Gwamnoni 3 da wasu fitattun 'yan Najeriya 5 da suka kamu da korona a makon da ya gabata

Sama da mutum 28,000 ne a Najeriya suka kamu da cutar korona yayin da sama da mutum 11,000 suka warke a halin yanzu.

A kalla an samu mutum 4,000 da suka harbu da kwayar cutar a makon da ya gabata. Wasu daga ciki sun hada da gwamnoni, hadimansu da kuma 'yan uwansu.

Da yawa daga cikin wadanda suka kamu basu nuna wata alamar cutar ba kuma sun killace kansu kamar yadda hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) ta bukata.

Gwamnoni 3 da wasu fitattun 'yan Najeriya 5 da suka kamu da korona a makon da ya gabata
Gwamnoni 3 da wasu fitattun 'yan Najeriya 5 da suka kamu da korona a makon da ya gabata Hoto: Healthwise
Asali: UGC

Jaridar Premium Time ta dubo fitattun 'yan Najeriya 8 da suka sanar da kamuwarsu da muguwar cutar a makon da ya gabata.

1. Gwamnan Ondo

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya sanar da kamuwarsa da cutar korona a ranar Talata da ta gabata.

Ya ce babu wata alamar cutar da ta bayyana amma ya killace kansa. Ya ce duk da hakan, babu aikin jihar da zai tsaya.

2. Gwamnan Ebonyi

A ranar Asabar, Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya sanar da kamuwarsa da muguwar cutar numfashin.

Ya tabbatar da cewa babu wata alamar cutar da ta fara bayyana amma ya killace kansa kamar yadda NCDC ta bukata.

Ya ce ya mika ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Kelechi Igwe. Ya sanar da cewa wasu daga cikin hadimansa masu kusanci da shi sun harbu.

3. Gwamna Okowa

Gwamna jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya harbu da cutar. A makon da ya gabata ya killace kansa bayan daya daga cikin diyarsa ta kamu.

4. Edith Okowa

Uwargidar gwamnan jihar Delta, Edith Okowa ma ta harbu da cutar

5. Matar gwamnan Benue

Matar Gwamnan jihar Benue, Eunice Ortom a ranar Juma'a ta sanar da kamuwarta da muguwar cutar.

A wata takarda da matar gwamnan ta sa hannu, ta ce danta da wasu ma'aikatan gidan gwamnatin duk sun harbu.

6. Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Osun

Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Osun, Wole Oyebamiji a ranar Talata ya harbu da cutar korona.

Oyebamiji da wasu mutum 10 sun harbu da cutar a ranar Talata.

Kwamishinan lafiya na jihar, Rafi Isamotu, ya danganta hakan da rashin kiyaye dokokin dakile cutar da jama'ar jihar ke yi.

7. Shugaban ma'aikatan fadar gwamnan jihar Jos

Noel Donjur, shugaban ma'aikatan fadar gwamnan jihar Jos ya harbu da muguwar cutar coronavirus.

Kamar yadda kwamishinan yada labarai na jihar, Dan Manjang ya sanar, ya ce Donjour bai bayyana alamun cutar ba.

Manjang ya ce dukkan jami'an da suka yi ma'amala da shi sun tafi gwaji sannan an killace shi kamar yadda NCDC ta bukata.

8. Shugaban ma'aikatan lafiyar asibitin koyarwa na Akure, jihar Ondo

An samu wannan sanarwar ne bayan sa'o'i kadan da mutuwar kwamishinan lafiya na jihar, Wahab Adegbenro, wanda ya rasu sakamakon annobar Coronavirus a ranar Alhamis.

A halin yanzu, yana killace inda yake karbar magani tare da jinya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel