Harbo jirgin UN: Majalisar dinkin duniya ta bukaci bincike da hukunci

Harbo jirgin UN: Majalisar dinkin duniya ta bukaci bincike da hukunci

- Majalisar dinkin duniya ta yi Alla-wadai da harin da aka kai wa daya daga cikin jiragenta a yankin Damasak da ke Borno

- Lamarin ya faru ne a ranar 2 ga watan Yuli wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyu da ya hada da yaro mai shekaru biyar

- Majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta bincike tare da daukar mataki a kam hakan

Majalisar dinkin duniya ta kushe harin da aka kai wa daya daga cikin jiragenta a yankin Damasak da ke Borno.

Mummunan al'amarin ya faru ne a ranar 2 ga watan Yuli wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyu da ya hada da yaro mai shekaru biyar.

A don haka, majalisar dinkin duniya ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta bincike tare da daukar mataki a kam hakan.

Harbo jirgin UN: Majalisar dinkin duniya ta bukaci bincike da hukunci
Harbo jirgin UN: Majalisar dinkin duniya ta bukaci bincike da hukunci Hoto: Wikimedia Commons
Asali: UGC

A wata takarda da majalisar ya fitar a ranar Asabar kuma shugaban kula da walwala tare da jin dadi na majalisar a Najeriya, Edward Kallon, yasa hannu, ya ce harsasan da mayakan suka sakarwa jirgin saman ne ya kabo shi tare da illa ga ayyukansu a yankin.

KU KARANTA KUMA: Tsige shugaban APC: Jama’a sun dasa ayar tambaya a kan rashin jin doriyar matar Oshiomhole

Kallon ya ce, “Ina bakin cikin sanar da cewar an harba wa jirgin agaji na majalisar dinkin duniya harsasai a lokacin harin. Babu ma'aikacin taimako da ke jirgin kuma matukan duk sun sauka lafiya.

"Tunanina na tare da matukan kuma na jinjina musu da yadda suka sauka duk da halin da jirgin yake ciki.

"Harin da barnar da aka yi ga jirgin ya matukar shafar aikin majalisar na samar da tallafi ga mazauna yankunan karkarar.

"Na yi matukar kushe harin kuma ina kira ga 'yan ta'addan da su kiyaye dokokin kare hakkin dan Adam tare da tabbatar da cewa sun kiyaye hakkin farar hula.

"Ina kira ga hukumomi a Najeriya da su tabbatar da tsaro tare da kariya ga dukkan ma'aikatan tabbatar da walwala da tallafi.

"Ina kara kira ga gwamnatin da ta tsananta bincike tare da yin adalci a kan abinda ya faru.

"Ina mika ta'aziyyata ga iyalan farar hular da suka rasa rayukansu tare da fatan samun lafiya ga wadanda suka samu raunika."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng