Zamani: Yarinya mai shekaru 14 ta gudu daga gidan iyayenta zuwa wurin saurayin 'facebook'

Zamani: Yarinya mai shekaru 14 ta gudu daga gidan iyayenta zuwa wurin saurayin 'facebook'

Wata yarinya 'yar shekaru 14 ta gudu daga gidan iyayenta da ke Biogbolo a karamar hukumar Yenagoa ta jihar Bayelsa domin kasancewa tare da saurayinta, Victory Age, mai shekaru 17 wanda suka hadu a dandalin sada zumunta na 'Facebook'.

Sai dai, rundunar 'yan sanda ta yi nasarar kama Age tare da abokansa tare da yin holinsu a hedikwatar rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa da ke Yenogoa a ranar Alhamis.

Rundunar 'yan sanda tana zargin matashin mai shekaru 17 da laifin boye yarinyar mai shekaru 14 na tsawon wata guda ba tare da izinin iyayenta ba.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa karamar yarinyar ta zabi guduwa zuwa wurin saurayin ne saboda mugun zaman da ke tsakaninta da matar mahaifinta.

Yarinyar, 'yar aji 4 a makarantar sakandire, ta ce ba ta sanar da kowa ba kafin ta bar gida, kawai ta bar rubutaccen sakone a dakinta kafin ta tafi.

Ta amince cewa Age da abokinsa suna kwanciya tare da ita a tsawon zamansu na wata guda, ta bayyana cewa ba tilasta mata suke yi ba, da amincewarta ake yin komai.

Zamani: Yarinya mai shekaru 14 ta gudu daga gidan iyayenta zuwa wurin saurayin 'facebook'
Zamani: Yarinya mai shekaru 14 ta gudu daga gidan iyayenta zuwa wurin saurayin 'facebook'
Asali: Facebook

"Na ziyarci abokina a Onopa bayan haduwarmu a 'Facebook'.

"Shi kansa ya girgiza da ya ganni da jakar kayana. Ya tambayeni me yasa na dauko jakar kaya, sannan me nake nufi?, nan take na bashi amsar cewa zan zauna tare da shi na tsawon sati guda.

"Ya tambayeni ko iyayena ba za su nemeni ba, sai na ce 'Eh'. Daga nan sai muka tafi wani Otal inda mu ka zauna na tsawon kwanaki uku kafin daga nan mu koma wurin abokinsa.

DUBA WANNAN: Takaicin kwace babur: Dan achaba ya cinnawa kansa wuta a ofishin 'yan sanda

"Abokinsa ne ya daukeni ya kaini Azikoro, inda na shafe tsawon wata guda tare da su.

"Shekaruna 14. Na kwanta da shi da abokinsa na tsawon wata guda. Ba su tilasta min saduwa da su ba, na sadu da su ne bisa amincewa da kuma niyyata," a cewarta.

A nasa bangaren, Age ya bayyana cewa; "lokacin da ta zo da 'yan kudi a jikina kuma ina tare da abokina, Gospel, wanda tare da shi mu ka je Otal muka kama daki.

"Na zauna a Otal tare da ita na tsawon kwanaki biyu kafin na koma gida. Kafin na tafi, sai da na shawarceta ta koma gida, saboda 'yan kudin aljihuna sun kare.

"Ban san me ya faru ba bayan nan. Na sadu da ita sau uku, daga nan kuma sai abokina, Gospel, ya dora; suka cigaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel