Mun gano aikin da APC ke son Ganduje ya yi mata a zaben jihar Edo - PDP

Mun gano aikin da APC ke son Ganduje ya yi mata a zaben jihar Edo - PDP

Jam'iyyar PDP ta ce ta bankado makircin da jam'iyyar APC ke son shiryawa a zaben kujerar gwamnan jihar Edo ta hanyar amfani da gwamnoninta guda uku; Dakta Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Hope Uzodinma na jihar Imo da Yahaya Bello na jihar Kogi.

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta tsayar da ranar 19 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a kada kuri'a a zaben kujerar gwamnan jihar Edo.

A cikin wani jawabi da kakakin jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, ya fitar, PDP ta ce tana sane da manufar jam'iyyar APC na zaben gwamnonin uku saboda "tana son hada irin rikicin da suka yi amfani da shi wajen yin fashin kujerar gwamna a jihar Kano da Kogi da Imo".

PDP ta ce tana tausayawa APC saboda ta rasa wanda za ta bawa shugabancin kwamitin yakin zaben gwamnan jihar Edo sai "mutumin da duk duniya ta shaida cewa ya yi abin kunya bayan an ganshi a cikin faifan bidiyo ya na cusa cin hancin makudan daloli a cikin aljihun babbar rigarsa.

"Sannan, shi wannan mutum bashi da mataimaki sai mutumin da bai san komai ba bayan kulla makircin kwace zabe, kamar yadda ya kulla makirci har kotun koli ta kwace kujerar gwamna ta damka masa.

"Duk hakan ba ta isa ba, sai da suka hada da gwamnan da ya yi amfani da jirgin sama mai saukar ungulu da 'yan daba da muggan makamai domin firgita ma su kada kuri'a domin a samu damar tafka magudi yayin zabensa a karo na biyu.

Mun gano aikin da APC ke son Ganduje ya yi mata a zaben jihar Edo - PDP
Ganduje
Asali: Twitter

"Mun san daga cikin shirin jam'iyyar APC na tunkarar zaben gwamnan jihar Edo akwai shirin amfani da wasu balagurbin ma su sa ido a kan harkar zabe domin a firgita jama'a, a take musu 'yancinsu na zaben dan takarar da suke so.

DUBA WANNAN: 2023: Shehu Sani, Dangiwa da sauransu sun yi martani a kan yunkurin kafa sabuwar jam'iyya

"A yayin da mu ke da dantakarar da jama'ar jihar Edo ke goyon bayansa, APC ta tsayar da dan takarar da bashi da wani abu da zai ja hankalin ma su zabe, hasali ma sun kira shi da 'barawo' a baya.

"Saboda sun fuskanci basu da dan takara mai nagarta, shine suka kafa kwamitin yakin neman zabe na mutanen da suka yi kaurin suna wajen tafka magudin zabe ta hanyar amfani da ta'addanci.

"Jam'iyyarmu tana son jan hankalin jam'iyyar APC a kan ta sani cewa "Gandollar", ''gwamnan kotun koli'' da "gwamna mai sa a harba bindiga daga jirgin sama don firgita ma su zabe'' ba zasu iya firgitamu ko su murkushemu su kwaci zabe a hannumu ba," a cewar jawabin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel