Takaicin kwace babur: Dan achaba ya cinnawa kansa wuta a ofishin 'yan sanda
Takaici, fushi da zugar zuciya sun tunxura wani dan achaba mai suna Husseini Walugembe ya cinnawa kansa wuta a ofishin jami'an rundunar 'yan sandan da suka kwace ma sa babur.
Walugembe, dan achaba a kasar Uganda, ya mutu nan take sakamakon babbakewar da ya yi bayan ya cinnawa kansa wuta domin nuna fushinsa a kan kin sakin babur dinsa.
Rundunar 'yan sanda ta kama babur din Walugembe a hannun abokinsa da ya karbi babur din da sunan aro.
'Yan sanda sun kama abokin Walugembe sakamakon samunsa da laifin daukar fasinja bayan doka ta haramta goyon biyu a babur a matsayin daya daga cikin matakan yaki da annobar cutar korona.

Asali: Depositphotos
Takaici ya kama Walugembe bayan ya sha zarya zuwa ofishin 'yan sanda domin karbar babur dinsa amma hakan ta ci tura.
DUBA WANNAN: Korona: Ya kamata mu daina wannan mugun wasan, jama'a suna shan wahala - Gamnan APC
Dan achabar ya ziyarci ofishin 'yan sanda da fetur dinsa a cikin wata kwalbar ruwa, sannan ya kulle kansa a cikin wani daki a harabar ofisihin, ya zuba fetur a jikinsa, sannan ya cinnawa kansa wuta.
Rundunar 'yan sandan kasar Uganda ta ce ta fara gudanar da bincike a kan zargin da ake yiwa jami'anta na karbar na goro kafin su saki ababen hawan da suka kama.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng