Yadda 'yan Boko Haram ke samun makamai – Majiya daga Rundunar Soji

Yadda 'yan Boko Haram ke samun makamai – Majiya daga Rundunar Soji

Wata majiya daga rundunar sojojin Najeriya ta ce Boko Haram suna samun makamai da motocci ne yayin harin da suke kai wa sansanin sojoji a yankin Arewa maso Gabas.

Rundunar ta bayyana hakan ne yayin mayar da martani a kan ikirarin da kakakin rundunar tsaro, Manjo Janar John Enenche ya yi na cewa rundunar soji ba ta san wadanda ke daukan nauyin 'yan ta'adda ba da inda suke samo makamai.

"Ba gaskiya bane a ce makaman da 'yan ta'addan ke amfani da shi yana da banbanci da wadanda muka siyo," a cewar daya daga cikin majiyar.

Yadda 'yan Boko Haram ke samun makamai
Yadda 'yan Boko Haram ke samun makamai. Hoto daga Folio.ca
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An kama wani mutum da ya yi wa 'yarsa ciki a Adamawa

"Maganar gaskiya shine mafi yawancin motocin, tankunan yaki da sauran makamansu daga sansanin mu suka sace. Idan kana iya tunawa, su kan sace makamai daga sansanin mu da suka kai hari. Yawancin motocin da suke amfani da shi daga wurin dakarun mu suka sace.

"Kuma suna samun makamai daga kasashen da muke makwabtaka da su na kusa da yankin tafkin Chadi a farashi mai rahusa. Safarar makamai daga yankin Tafkin Chadi yana da sauki saboda rashin tsaro a iyakoki," in ji majiyar.

Wani mai sharhi a kan al'amurran yau da kullum, Abubakar M. Kareto, ya ce 'yan ta'addan suna da hanyoyin samun kudade da dama da suka hada da karbar haraji daga mutanen kauyukan da suke kai hari, garkuwa da mutane da sace kaya a sansanin sojoji.

Manjo Janar Enenche, a ranar Alhamis yayin taron manema labarai a kan ayyukan sojojin ya ce rundunar sojin ba ta san wadanda ke daukan nauyin 'yan Boko Haram da sauran 'yan ta'adda ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan ikirarin ya ci karo da abinda shugabanin sojoji da fararen hula suke fadi a baya ba.

Misalin a shekarar 2015, Kwamandan Operation Lafiya Dole da ke Maiduguri, jihar Borno, Manji Janar Yushau Abubakar ya ce rundunar tana da jerin sunayen wadanda ke daukan nauyin 'yan ta'addan kuma za ta kawo karshen ta'addancin a karshen wannan shekarar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel