Dakarun soji sun halaka 'yan fashi biyu a Jos

Dakarun soji sun halaka 'yan fashi biyu a Jos

- Dakarun sojin rundunar Operation Safe Haven, sun kashe 'yan fashi da makami biyu a garin Jos

- Kamar yadda kwamandan rundunar, Manjo Janar Chukwuemeka Okonkwo ya bayyana, dakarun sun kai samame ne yankin Rock Haven

- Ya ce tuni mazauna yankin Rock Haven na karamar hukumar Jos ta arewa suke ta korafi a kan ayyukan 'yan fashin a yankin

Dakarun Operation Safe Haven a ranar Alhamsi sun kashe 'yan fashi da makami biyu a Jos, babban birnin jihar Filato.

Kamar yadda kwamandan OPSH, Manjo Janar Chukuemeka Okonkwo ya bayyana, wannan ya biyo bayan samamen da wasu 'yan rundunar suka kai yankin Rock Haven da ke karamar hukumar Jos ta arewa.

Ya ce bayan korafin da mazauna yankin suka yi na addabarsu da 'yan fashi da makami suka yi, sun yi musayar wuta da wadanda ake zargin wanda hakan yasa suka kashe biyu daga ciki.

Ya ce dakarun sun samu bindigogi biyu daga gawawwakin 'yan fashin.

Rundunar 'yan sandan jihar sun karba gawawwakin.

Dakarun soji sun halaka 'yan fashi biyu a Jos
Dakarun soji sun halaka 'yan fashi biyu a Jos. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Harkallar aiki 774,000: Sanata ya yi wa minsitan Buhari 'wankin babban bargo'

A wani labari na daban, Legit.ng ta ruwaito cewa, yaki da ta'addanci a ranar Alhamis, 2 ga Yuli, ya samu gagarumin nasara yayinda rundunar Operation Lafiya Dole sun ragargaza mabuyar yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.

A bidiyon da hedkwatar tsaro DHQ ta saki a shafin Tuwita ranar Juma'a, 3 ga Yuli, an yiwa yan ta'addan ruwan annaru ne a mabuyarsu dake Mainyakare, cikin dajin Sambisa.

A harin, an kona gidajensu kuma yan Boko Haram da dama sun rasa rayukansu.

Jawabin yace: "Dakarun mayakan saman rundunar Operation Lafiya Dole sun ragargaza wurin ganawar yan ta'addan Boko Haram, gidajensu da kuma hallaka mayakan a Mainyakare, a cikin dajin Sambisa dake jihar Borno."

"An kai wannan harin sama ne jiya, 2 ga Yuli, 2020.

"Jirgin farko ya jefa Bam dai-dai inda ake bukata kuma ya ragargaza shi. Daga baya sauran jiragen suka babbaka sauran gine-ginen da aka nufi kai hari. An kashe yan ta'addan Boko Haram sakamakon hakan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel