COVID-19: Ban taba samun gudumuwar kudi daga gwamnatin tarayya ba - Emmanuel

COVID-19: Ban taba samun gudumuwar kudi daga gwamnatin tarayya ba - Emmanuel

Gwamna Udom Emmanuel ya ce gwamnatin jihar Akwa Ibom ba ta samu wani tallafin kudi daga wajen gwamnatin tarayya wajen yaki da annobar cutar COVID-19 ba.

Mai girma gwamnan ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi wata hira da ‘yan jarida kamar yadda ya saba, domin yi wa mutanen jiharsa bayanin inda aka kwana wajen yakar annobar.

Udom Emmanuel ya ke cewa akwai bukatar ya fadawa mutane gaskiyar halin da ake ciki, ganin cewa wasu sun fara jita-jitar cewa gwamnatin tarayya ta ba jihar Akwa Ibom gudumuwar kudi.

“Har yanzu da na ke magana, ban samu ko da Naira daya daga gwamnatin tarayya domin yaki da COVID-19 ba. Mutane da-dama su na tunanin mu na aikin nan ne saboda kudin da gwamnatin tarayya ta ba mu.”

“Ko kusa ba haka ba ne. Mu na yin wannan aiki ne domin hakkin kare rayukan jama’a ya na kanmu. Ni ne zan zama kan gaba wajen yaki da wannan annoba.” Inji Udom Emmanuel.

KU KARANTA: COVID-19 ta harbi mutane 600 a Najeriya

COVID-19: Ban taba samun gudumuwa daga gwamnatin tarayya ba - Emmanuel
Gwamna Udom Emmanuel Hoto: Akwa Ibom
Asali: Facebook

Gwamnan ya shaidawa mutanensa cewa nauyin kare rayuka ba a kan wuyansa da malaman lafiya, da jami’an gwamnati kurum ya rataya ba. Ya ce dole sai mutanen gari sun tashi tsaye.

Emmanuel ya yi amfani da wannan dama ya godewa kungiyoyin da ke aikin ganin karshen annobar a jihar. “Idan Ubangiji bai kawo karshen wannan ba, dole mu yi addu’a, mu nemi hanyar da za mu tsira.

“Bari in yabawa malaman lafiyarmu, kungiyar CAN, ‘yan siyasa da sauran ‘yan kasa da su ka fahimce mu, su ka bamu hadin-kai a wannan lokaci. Ina godewa wadanda su ke bin doka, da ma wadanda ba su bi, da ma’aikatan kwana-kwana da jami’an tsaro da su ke namijin kokari.”

Mista Emmanuel ya ce akwai wani ‘dan adawar gwamnatinsa wanda cutar ta kama, a karshe aka yi masa magani har ya mike bayan ya gama sukar gwamnati. Gwamnan ya kuma yi kira ga jama’a su bi doka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng