COVID-19: 'Yan majalisa 4 sun fara ciwo, sun ki zuwa gwaji duk da suna bidiyon Akeredolu

COVID-19: 'Yan majalisa 4 sun fara ciwo, sun ki zuwa gwaji duk da suna bidiyon Akeredolu

Hudu daga cikin ‘yan majalisar jihar Ondo 19 suna fama da matsananciyar rashin lafiya bayan sun raka Gwamna Rotimi Akeredolu zuwa Abuja, wata majiya ta sanar.

A ranar 16 ga watan Yuni, Akeredolu da ke bukatar zarcewa ya je Abuja don bayyana bukatarsa tare da siyan fom a sakateriya APC ta kasa da ke Abuja.

Kafin ya garzaya hedkwatar jam’iyyar ta kasa, an ga gwamnan tsakiyan ‘yan majalisa inda suke rera masa wakoki.

“Kaine wanda Ubangiji yace, kaine mai nasara ba za ka fadi ba. Kaine wanda Ubangiji ya ce,” suka rera masa.

Daga gwamnan har ‘yan majalisan babu wanda ya kiyaye dokokin kare kai na hukumar hana yaduwar cututtuka ta NCDC.

Basu saka takunkumin fuska ba kuma basu kiyaye dokokin nesa-nesa da juna ba a wani bidiyonsu da ya shiga kafofin sada zumuntar zamani.

COVID-19: 'Yan majalisa 4 sun fara ciwo, sun ki zuwa gwaji duk da suna bidiyon Akeredolu
COVID-19: 'Yan majalisa 4 sun fara ciwo, sun ki zuwa gwaji duk da suna bidiyon Akeredolu Hoto: Punch
Asali: Twitter

Jim kadan bayan Akeredolu ya yi atishawa a tafin hannunsa, daya daga cikin ‘yan majalisar ya kama hannun inda ya daga shi sama don godiya ga sauran ‘yan majalisar, lamarin da yasa gwamnan ya yi murmushi.

Bayan makonni biyu, gwamnan ya sanar da cewa ya kamu da muguwar cutar korona kuma ya bai wa dukkan makusantansa umarnin killace kansu sannan su yi gwaji.

Wani hadimin dan majalisar jihar ya sanar da The Cable cewa duk da ‘yan majalisar basu gabatar da kansu don gwaji ba, hudu daga cikinsu basu da lafiya kuma sun daina fita tun makon da ya gabata.

KU KARANTA KUMA: Kun ci amanar Sardauna - Gwamna Yahaya Bello ya caccaki dattawan arewa

“Ko kafin gwamnan ya bada sanarwa a ranar Talata, Olugbenga Omole, kakakin daya daga cikin ‘yan majalisa da wasu ‘yan majalisa uku basu da lafiya,” majiyar tace.

“Abun takaici ne yadda suka nuna ba za su je gwajin COVID-19 ba saboda suna tsoro. Suna yi kamar wasu kauyawa.

“Babu wanda ya tsallake cutar a jihar Ondo. Hatta matar gwamnan na ji an ce ta kamu da cutar,” in ji majiyar.

Amma kuma hara yanzu ba a tabbatar da cewa matar gwamnan ta kamu da muguwar cutar da ta zama ruwan dare ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel