Strike Force: Kwastam sun tara N1.1b daga Junairu zuwa Yuni a 2020 a Kudu maso Yamma

Strike Force: Kwastam sun tara N1.1b daga Junairu zuwa Yuni a 2020 a Kudu maso Yamma

Dakarun Strike Force na hukumar kwastam masu yaki da fasa-kauri a Najeriya sun yi nasarar samun fiye da Naira biliyan daya a hannun maso shigo da kaya daga kasashen waje.

A cikin watanni shida da su ka wuce, jami’an na kwastam sun samu N1.104b daga ‘yan kasuwan da ke shigo da kaya ta jiragen ruwa ba tare da sun biya gwamnati harajin da ya kamata ba.

Wasu ‘yan kasuwa su kan shigo da kaya zuwa Najeriya a boye domin gujewa biyan kudin kaya.

Hukumar kwastam ta samu wannan kudi ne a wajen irin wadannan ‘yan kasuwa da su ke kin biyan gwamnati kudinta bayan sun shigo da kaya ta iyakokin Kudu maso yamma.

Wani babban jami’in hukumar kwastam, Abba Kakudi ya shaidawa jaridar The Nation, a iyakokin Kudu maso yammacin kasar, an samu wadanda ba su biyan cikakken kudin shigo da kaya.

An yi lissafin kudin da hukumar ta samu ne daga 1 ga watan Junairu zuwa ranar 11 ga watan Yunin bana. Jami’in ya ce duk da ana fama da annobar COVID-19, sun iya samun Biliyan guda.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace mutane a Jihar Nasarawa

Strike Force: Jami’an kwastam sun tara N1.1b daga Junairu zuwa Yuni a 2020
Shugaban hukumar kwastam
Asali: Facebook

A cikin makonni biyun da su ka wuce, dakarun kwastam sun koyawa masu fasa-kauri hankali inji Abba Kakudi.

Masu shigowa da kaya ta barauniyar hanya su na yi wa tattalin arzikin Najeriya barazana ta hanyar ragewa kasar kudin shiga da kuma dawo da hannun agogon manufofin gwamnati baya.

“Daga cikin kayan da ma’aikatan su ka karbe akwai buhuna 1000 na shinkafa masu nauyin 50kg wadanda aka biyawa kudin shiga (DPV) na Naira miliyan 13.252, gwanjon motoci 10 da aka karbi Naira miliyan 31.185 a kansu, da DPV na Naira miliyan 2.16 a kan gwajon tufafi”

Kwastam ta ce babu bukatar shigo da wadannan kaya da ake samu a Najeriya. Jami’in ya ce ana samun wasu masu fasa kauri dauke da lakanin asiri da layoyi da makamai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel