COVID-19: Jami'an kwastam 10 sun kamu da korona a jihar Legas

COVID-19: Jami'an kwastam 10 sun kamu da korona a jihar Legas

- Shugaban hukumar kwastam na yankin Apapa, Mohammed Abba-Kura, ya bayyana cewa jami'ansu 10 sun harbu da annobar korona

- Mohammed Abba-Kura ya tabbatar da cewar dukkaninsu sun warke a yanzu bayan jinya da suka yi asibitin jami'ar Lagas

- Ya jama'a da su kiyaye tsafta yayin gudanar da ayyuka a tashoshin jiragen ruwan

Shugaban hukumar kwastam na yankin Apapa, Mohammed Abba-Kura, a ranar Alhamis ya ce jami'ansu 10 sun harbu da muguwar cutar korona kuma an warkar da su asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas.

Hakan ya kasance ne duk da shugaban hukumar ya bayyana da cewa duk wani abu da ya danganci tsaron lafiya ba zai shiga ko fita ba har sai cibiyoyin gwamnati sun aminta.

A yayin jawabi ga manema labarai a ofishinsa a ranar Alhamis, Mohammed Abba-Kura ya yi bayanin cewa babu yadda hukumar za ta hana duba kaya a halin yanzu saboda tsoron annobar korona.

COVID-19: Jami'an kwastam 10 sun kamu da korona a jihar Legas
COVID-19: Jami'an kwastam 10 sun kamu da korona a jihar Legas Hoto: Tribune
Asali: UGC

Amma ya ce akwai bukatar jama'a su kiyaye tsafta yayin gudanar da ayyuka a tashoshin jiragen ruwan, jaridar Tribune Online ta ruwaito.

A cewar Abba-Kura, "A lokacin da jami'aina biyu suka harbu da cutar, na bai wa sauran umarnin zuwa gwaji kuma daga baya an gano karin mutum takwas.

"Duk sun warke a asibitin LUTH kuma an sallamesu. Yana da muhimmanci matuka idan jama'a suka kiyaye tsafta a yayin da suke aiki.

"Kalli wannan takunkumin fuska, kamata yayi a jefar da shi bayan amfani da shi amma sai ka ga ana daukar kwanaki ana amfani da shi.

"Da yawa daga cikin jami'aina an wayar musu da kai a zuwan da likitoci suka yi daga hedkwatar kwastam ta kasa da ke Abuja."

KU KARANTA KUMA: Sunaye: Buhari ya rantsar da shugaba, mambobin hukumomin FCC da RMAFC

Kamar yadda hukumar ta bayyana, jiragen ruwa 13 ne suka ziyarci kasashen da cutar korona ta yawaita.

Shugaban ya ce duk wani jirgin ruwa da hakan ta faru da shi, jami'ansa ba za su kusancesa ba har sai cibiyar da ke da alaka da shi ta tabbatar da lafiyar komai.

A bangaren samun kudin shiga, ya bayyana cewa sun samu N52.369 biliyan daga fitar da kaya da kuma N227.347 na kudin shiga tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel