Sunaye: Buhari ya rantsar da shugaba, mambobin hukumomin FCC da RMAFC

Sunaye: Buhari ya rantsar da shugaba, mambobin hukumomin FCC da RMAFC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, ya rantsa da sabon shugaban hukumar tabbatar da daidaito a rabon mukamai da guraben aiyukan gwamnatin tarayya, Muheeba Dankaka daga jihar Kwara, da kuma wasu mambobin hukumar su 36.

Shugaban kasar ya kuma rantsar da Kwamishinonin tarayya na hukumar tattara kudaden shiga (RMAFC) su shida, ciki harda Gboyega Oladele daga Osun.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Buhari ya kuma rantsar da sabbin sakatarorin dindindin su hudu da kuma mambobin hukumar ma’aikatan gwamnati su biyu.

Sunaye: Buhari ya rantsar da shugaba, mambobin hukumomin FCC da RMAFC
Sunaye: Buhari ya rantsar da shugaba, mambobin hukumomin FCC da RMAFC Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Hadimin shugaban kasar, Buhari Sallau ma ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoraci rantsar da shugaban hukumar tabbatar da daidaito a rabon mukamai da guraben aiyukan gwamnatin tarayya, kwamishinonin hukumar tattara kudaden shiga a fadar shuaban kasa a ranar 2 ga watan Yuli."

Mambobin hukumar FCC 36 sun hada da Ogbulogo (Abia), Salihu Bello (Adamawa), Dorah Daniel (Akwa-Ibom), Ibeabuchi Uche, (Anambra), Mohammed Tijjani, (Bauchi), Tonye Okio (Bayelsa) da Silas Macikpah (Benue).

Sauran sune Abba Ali Monguno (Borno), Nsor Atamgba (Cross River), Alims Agoda (Delta), Tobias Chukuemeka (Ebonyi), Imuetinyan Festus (Edo), Sesan Fatoba (Ekiti), Ginika Tor (Enugu). Hamza Mohammed (Gombe), Diogu Uche, (Imo) da Lawan Ya’u Roni (Jigawa).

Hadiza Muazu (Kaduna), Mohammed Na’iya (Kano), Lawal Garba (Katsina), Abubakar Atiku Bunu (Kebbi), Idris Bello (Kogi), Are Bolaji (Lagos), Nasir Isa Kwarra (Nasarawa), da Suleiman Barau (Niger).

Sauran da aka rantsar sune Abiodun Akinlade (Ogun), Olufemi Omosanya (Ondo), Adeoye Olalekan (Osun) Adeniyi Olowofela (Oyo), Stephen Jings (Plateau), Wokocha Augustine (Rivers),

Har ila yau an rantsar da Abdullahi Tafida (Sokoto), Alhaji Armaya’u Abubakar (Taraba), Jibril Maigari (Yobe), Sani Garba (Zamfara) da kuma Adamu Sidi-Ali (babbar birnin tarayya).

Har ila yau Buhari ya nada Idahagbon Henry a matsayin kwamishina mai wakiltan Jihohin Edo, Ekiti da Ondo a hukumar ma’aikatan gwamnati.

Nadin na kunshe ne a wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanto a ranar Laraba.

Ya ce nadin ya yi daidai da tanadin sashi na 154(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Shugaban kasar ya aika wasika inda ya nemi majalisa ta tabbatar da nadin.

A wata wasikar kuma, Shugaban kasar ya nemi a tabbatar da nadin Usman Hassan a matsayin kwamishina mai wakiltan jihar Kaduna a hukumar tattara kudaden shiga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel