Shugaban kasa Buhari ya amince da wasu ayyukan N20.36b wajen taron FEC

Shugaban kasa Buhari ya amince da wasu ayyukan N20.36b wajen taron FEC

A wajen taron FEC da ake yi kowane mako, gwamnatin tarayya ta amince da ware kudi N20, 366, 454, 990 domin yin wasu ayyuka na gyara hanyoyi da wani titin jirgin sama a zaman jiya.

Gwamnatin tarayya za ta kashe wannan kudi ne a ma’aikatu hudu kamar yadda mu ka samu labari daga gidajen jaridun Najeriya a ranar Laraba, 1 ga watan Yulin 2020.

Bayan an kammala ganawar shugaban kasa Muhammadu Buhari da jami’an gwamnatinsa, wasu Ministoci sun bayyyana cewa takardun da su ka gabatar a majalisar FEC sun samu shiga.

Ministar ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola; Ministan babban birnin tarayya, Mohammed Bello; Ministan harkar ruwa, Suleiman Adamu da ministan harkokin jiragen sama, Hadi Sirika, su ka bayyana wannan.

Mohammed Bello ya ce an yi na’am da wasu takardu biyu da ya gabatar gaban shugaban kasa na yin titi daga Yaba zuwa Gurdi a cikin yankin Abaji da kuma aikin hanyoyi a cikin garin Abaji.

Ministan babban birnin tarayyar ya ke cewa: “Aikin farkon kwangila ce za a bada na yin titi da zai hada Yaba da Gurdi a Abaji a kan N4, 648, 255, 381.42 da sa ran za a kammaka cikin watanni 20.”

KU KARANTA: A daina yi wa shafaffu da mai alfarma wajen neman aiki - Buhari

Shugaban kasa Buhari ya amince da wasu ayyukan N20.36b wajen taron FEC
Shugaban kasa Buhari da Ministoci a taron FEC
Asali: Twitter

“Kwangila na biyun aikin tituna ne a garin Abaji da ke kudancin birnin tarayya. Titunan sun kai tssawon kusan kilomita 8.4, za su ci N2, 128, 176,102.50, ana sa rai a gama cikin watanni shida.” inji Bello.

Sanata Hadi Sirika ya ce gwamnatin tarayya ta amince da aikin hanyar motocin haya a cikin babban filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas. Aikin zai ci Naira biliyan 2.3

Ma’aikatar ruwa ta gabatar da takardun neman kwangilar gyara cibiyar noman rani da ke garin Lankang, jihar Filato. FEC ta amince da wannan kwangila a kan Naira miliyan 634.2.

Babatunde Fasola ya gabatar da takardu biyu ne wadanda duk aka amince da su. “Takardar farko aikin titi ne na iyakar Koton-Karfe-Lokoja na hanyar Abuja-Abaji-Lokoja a kan Billiyan 3.076.”

“Na biyu kuma titin Cham-Numan ne a kan babban hanyar Gombe-Yola. Wannan aiki zai ci Biliyan 7.607.” Gaba daya wadannan ayyuka da za ayi, za su tashi a kusan Naira biliyan 20.4

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel