IPPIS: BUK ta mayar da lakcarorin da ta kora bakin aiki

IPPIS: BUK ta mayar da lakcarorin da ta kora bakin aiki

Jami'ar Bayero da ke Kano; wato BUK, ta mayar da wasu lakcarori bakin aikinsu bayan a baya ta sallamesu daga aiki saboda sabon tsarin biyan albashi (IPPIS) da gwamnatin tarayya ta bullo da shi.

Bayan gwamnatin tarayya ta tilasta malaman jami'o'i shiga tsarin IPPIS ne jami'ar BUK ta sallami lackcarorin daga aiki saboda su na aiki ne bisa tsarin kwangila.

Jami'o'i ne ke biyan lakcarorin da ke aiki a bisa tsarin kwangila daga kudaden aljihunsu.

IPPIS tsarin biyan albashi ne na ma'aikatan da gwamnatin tarayya ta dauka aiki kuma ta ke biyansu daga aljihunta, a saboda haka tsarin ba zai karbi ma su aiki bisa tsarin kwangila ba.

BUK ta sallami lakcarorin daga aiki a ranar 10 ga watan Yuni bayan gwamnatin tarayya ta kafe a kan cewa tilas sai dukkan malaman jami'o'in gwamnatin tarayya sun shiga tsarin IPPIS.

Daya daga cikin lakcarorin da aka sallama, Dakta Sa'idu Ahmad Dukawa, ya shaidawa jaridar HumAngle cewa jami'ar BUK ta kira shi kuma ta mayar da shi bakin aikinsa.

Ya bayyana cewa hukumar jami'ar ta kira shi ranar Litinin 2 sanna ta janye takardar gimtse aikinsa na kwangila da ta damka ma sa a baya.

IPPIS: BUK ta mayar da lakcarorin da ta kora bakin aiki
Kofar shiga sabon ginin jam'iar BUK
Asali: UGC

Dukawa ya ce an sanar da su cewa gwamnatin tarayya ta nuna niyyarta na cigaba da biyan albashinsu.

"Eh, tabbas jami'ar BUK ta aiko min da takardar kiranye. An sanar da mu cewa an yi wa tsarin IPPIS gyaran da zai hada da lakcarorin da ke aiki bisa tsarin kwangila.

"Bisa wannan sabon tsari, jami'ar ta sake daukata aiki bisa tsarin kwangila na tsawon shekara biyu a kan sharuda da ka'idoji," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Suna da jiha: Buhari ya sake aikawa majalisa sabbin sunayen mutane 42 a matsayin jakadu

Shugaban jami'ar BUK, Farfesa Mohammed Yahuza Bello, ya tabbatar da hakan yayin da ya ke magana da manema labarai a daren ranar Talata.

Ya bayar da tabbacin cewa an mayar da dukkan sauran lakcarorin da jami'ar ta sallama bayan an yi gyara a tsarin IPPIS ta yadda gwamnatin tarayya za ta cigaba da biyan albashin malaman jami'a da ke aiki bisa tsarin kwangila.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel