Majalisar Shugaban kasa ta bukaci a daidaita farashin kudin kasashen waje a Najeriya

Majalisar Shugaban kasa ta bukaci a daidaita farashin kudin kasashen waje a Najeriya

Majalisar da ke ba shugaban Najeriya shawara a game da harkar tattalin arziki, PEAC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da farashi daya na kudin kasar waje a kasuwar canji.

PEAC ta bada wannan shawara ne domin a saukakawa ‘yan kasuwan da ke kasar kamar yadda Malam Garba Shehu ya bayyana. Hadimin shugaban kasar ya fitar da wannan jawabi ne a makon nan.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasar ya yaba da irin gudumuwa da taimakon da majalisar ta ke yi wa kasar. Shugaban ya bayyana kokarin PEAC a matsayin karantar da gwammnati domin fita daga halin kangi.

Da ya ke magana ta bidiyo da majalisar mashawartan na sa, shugaba Buhari ya ce: “Mu kasa ne da mu ka yi suna wajen yawan jama’a, da matsalar rashin kayan more rayuwa, da karancin gidaje da matsin tattalin arziki.”

Duk da wannan kuma sai ga shi annobar COVID-19 ta barke a kasar wanda ta yi mummunan tasiri ga karfin tattalin Najeriya a sanadiyyar karyewar farashin man fetur.

KU KARANTA: 'Yan kwamitin da za su sa ido wajen rabawa Matasa 774, 000 aiki

Majalisar Shugaban kasa ta bukaci a daidaita farashin kudin kasashen waje a Najeriya
Majalisar PEAC a fadar Shugaban kasa
Asali: Twitter

PEAC ta ji dadin yadda gwamnatin tarayya ta dauki wasu shawarwari da ta gabatar mata. Shugaban majalisar, Farfesa Doyin Salami ya yaba da yadda aka yi wa kasafin kudin 2020 da shirin MTEF garambawul.

Daga cikin shawarwarin da Doyin Salami da abokan aikinsa su ka ba shugaban kasar shi ne barin farashin man fetur a hannun ‘yan kasuwa, da dabbaka aikin kwamitin Oronsoye da gyara darajar Naira.

Har yanzu gwamnati ba ta kawo gyara a yadda ake saida kudin kasar waje ba, amma ta dauki mafi yawan shawararin da aka bada. Ana samun mabanbanta farashi tsakanin kasuwa da banki.

Farfesa Salami ya ce sai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi tsaye wajen ganin abubuwa su na tafiya daidai tsakanin ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnatin tarayya.

A jawabin majalisar, ta ce shirin da gwamnati ta ke yi na kashe Naira tiriliyan 2.3 zai iya zuwa da matsaloli. Salami ya ce hakan zai iya jawo farashin kaya su tashi, ko a batar da kudin a inda bai dace ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel