Yadda zan tsamo ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci - Buhari

Yadda zan tsamo ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 30 ga watan Yuni, a taron Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a shekaru 10 masu zuwa.

Shugaban kasar ya aika da jawabin ne a taron da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ta faifen bidiyo, inda aka kafa kungiyar yaki da fatara da talauci a duniya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa taron na yanar gizo ya kaddamar da kungiyar kasashe domin yaki da fatara da talauci a duniya wato APE.

Akalla akwai ‘yan Najeriya milIyan 94 wadanda ke fama da kangin talauci kamar yadda lissafin kididdigar Oxfam ta tabbatar.

Yadda zan tsamo ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci - Buhari
Yadda zan tsamo ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci - Buhari Hoto: Reuters
Asali: UGC

An samar da APE ne domin ya zama wani hanya da mambobin majalisar UN, kasa da kasa da sauran masu ruwa da tsaki za su tallafi matakan dakile talauci.

Buhari ya yi maraba da kafa wannan gagarumar kungiya, inda ya kara da cewa tuni dama Najeriya ta wuce kuma ta shige sahun gaba wajen yakar fatara da talauci, ta hanyar kafa shirin inganta rayuwa.

Ya ce: “Saboda mun dauki yakar fatara da talauci da gaske, shi ya sa da hawan gwamnatina na zango biyu a 2019, mu ka kafa shirin ceto ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci daga nan zuwa shekaru 10.

“Na yi imani cewa wannan shiri ne mai muhimmanci da zai kai mu ga ci. Har ma mu ka mike tsaye wajen inganta noma domin samun wadataccen abincin dogaro da kai.

“A saboda haka mun bijiro da tsare-tsare masu tarin yawa, har da shirin tallafa wa masu kananan masana’antu.”

KU KARANTA KUMA: Buhari: Najeriya na cikin mawuyacin halin rashin ci gaba

Shugaban kasar ya kuma bayyana shirin gwamnatinsa na kara kai’mi wajen ci gaban al’umma, wanda suka hada da zuba jari sosai a bangaren ilimi, musamman ilimin yara mata.

A baya mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kasar Najeriya na cikin mawuyacin hali na rashin ci gaba kuma tana bukatar a gyara alkiblar tattalin arzikinta.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 30 ga watan Yuni yayin da yayi taro da majalisar tattalin arziki ta kasa (PEAC).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel