Umar Farouk ya jinjinawa Buratai, Dakarun Sojoji, ya bada shawara kan sha'anin tsaro
Sarkin Daura, Mai martaba Dr. Umar Farouk Umar OON, ya yi magana game da halin da ake ciki na rashin tsaro, ya ce kalubalen da ake fuskanta a yau, ya zarce na lokacin yakin basasa.
Jaridar Vanguard ta ce ra’ayin Sarkin na Daura ya zo daidai da abin da kungiyoyi irinsu Ohanaeze Ndigbo, PANDEF, da Afenifere na Ibo, Neja-Delta da Yarbawa su ke fada game da halin da ake ciki.
Sarkin ya bayyana cewa hanyar kawo karshen wannan musiba da ake ciki ita ce a dage da addu’o’i da abin da ya dace kamar yadda aka ajiye banbancin ra’ayi, aka ga karshen rikicin Biyafara a baya.
A jawabinsa, Sarkin ya yaba da kokarin da sojoji su ke yi na ganin an samu zaman lafiya a Daura da fadin kasar tun bayan da Janar Tukur Buratai ya shiga ofis a matsayin hafsun sojoji.
Farouk Umar ya ce ya ji dadin irin aikin da Tukur Buratai ya ke yi, ya bukaci a ba sa goyon-baya.
Mai martaba Umar Farouk Umar ya yi wannan jawabi ne a lokacin da Laftana-Janar Tukur Yusuf Buratai ya kai wata ziyarar aiki zuwa garin Daura a jihar Katsina a karshen makon da ya wuce.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya koka da halin da Najeriya ta ke ciki
Shugaban hafsun sojojin ya yi amfani da wannan dama wajen gaida Sarkin Daura, inda ya bayyana masa shirin da bataliyar 171 na sojojin kasa su ke yi na kawo karshen ta’adin ‘yan bindiga.
Janar Tukur Buratai ya roki Mai martaban da mutanen garin Daura su sa sojojin kasa a addu’a. Ya ce Dakarun Najeriya za su kawo karshen matsalar rashin tsaron nan ba da dadewa ba.
Tukur Yusuf Buratai ya tabbatarwa masarautar mahaifar shugaban kasan Najeriya cewa sojoji za su zabura da zimmar magance matsalolin tsaro, musamman a yankin na Arewa maso yamma.
Sojan ya ce ya kawo wannan ziyara ne duba da ta’adin da ‘yan bindiga su ke yi a jihar Katsina.
“Yanzu sojojin Najeriya sun fara sauya tsare-tsare a fadin Najeriya, kuma manyan sojojin kasar sun zo jihar ne domin dabbaka umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada na magance matsalar rashin tsaro a kasar.” Inji Buratai.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng