Kwamitin su Folasade Tinubu-Ojo za ta zabi Matasa 20, 000 da za a dauka aiki a Jihar Legas

Kwamitin su Folasade Tinubu-Ojo za ta zabi Matasa 20, 000 da za a dauka aiki a Jihar Legas

Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitocin da za su jagoranci lura da matasa 774, 000 da za a dauka aikin wucin-gadi a daukacin kananan hukumomin da ake da su a fadin Najeriya.

A jihar Legas, jagororin wannan kwamiti sun hada da jagoran jam’iyyar APC Alhaji Mutiu Are, da kuma ‘diyar tsohon gwamnan jihar kuma shararren ‘dan siyasar Najeriya, Folasade Tinubu-Ojo.

Tinubu-Ojo wanda ita ce ta gaji lakabin Iyaloja-General bayan rasuwar mahaifiyar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta na cikin kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa.

Wannan kwamiti zai sa ido a kan yadda za a zakulo matasa 1, 000 a kowace karamar hukuma da ke Legas. Gwamnati za ta dauki hayar matasa 20, 000 a jihar mai kananan hukumomi 20.

Sauran ‘yan kwamitin sun hada da shugaban kungiyar NURTWA na direbobin haya na Legas, Musiliu Akinsanya wanda aka fi sani da MC Oluomo.

KU KARANTA: Minista: Babu wani wanda ya isa ya hana mu daukar matasa 774, 000 aiki

Kwamitin su Folasade Tinubu-Ojo za ta zabi Matasa 20, 000 da za a dauka aiki a Jihar Legas
Ministan kwadagon Najeriya, Festus Keyamo SAN
Asali: Facebook

Tsohon wata shugaban karamar hukuma a jihar, Kayode Elesin ya na cikin kwamitin. Ragowar ‘ya ‘yan kwamitin na mutane 20 sun hada da kwamishinoni irinsu Bamgbose Martins da Cornelius Ojelabi.

Wata shararriyar mace da ke cikin kwamitin ita ce jagorar mata ta jam’iyyar APC a Legas, Fadekemi Otitonaiye. Sauran matan kuma su ne Modupe Ola, da Serena Edward.

Jaridar Punch ta rahoto cewa na kusa da gwamna Babajide Sanwo-Olu kamar Mista Omotayo Oduntan-Oyelodun da Hon. Wale Adelana sun samu alfarmar shiga kwamitin.

Kwamitin na ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi ya na kunshe da masu sarauta uku da kuma Tajudeen Gbadamosi; Ashiru Olakunle, Labrar Folami, Olufeko Adebowale, da Akanni Babatunde.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel