Gwamnonin Najeriya 5 da suka kamu da cutar korona

Gwamnonin Najeriya 5 da suka kamu da cutar korona

Gwamnonin Najeriya biyar ne suka kamu da cutar COVID-19 tun bayan da annobar ta barke a kasar.

Ma’aikatar lafiya ta tarayya a ranar Juma’a, 28 ga watan Fabrairun 2020, ta tabbatar da mai dauke da cutar COVID-19 na farko a Lagas, mutumin wanda ya kasance dan kasar Italiya yana aiki ne a Najeriya kuma ya dawo ne daga Milan a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Annobar ya sa Najeriya ta zamo kasar Afrika ta uku da aka samu bullar utar bayan Algeria da Masar.

Sai dai kuma, yawan masu cutar na ta hauhawa duk da matakan da gwamnati ta dauka domin hana yaduwar cutar.

Cikin watanni hudu a jere, annobar ya kama sama da mutum 25,000 yayinda wasu manya da dama suka kamu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnonin Najeriya 5 da suka kamu da cutar korona
Gwamnonin Najeriya 5 da suka kamu da cutar korona Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Wadannan sune gwamnonin Najeriya biyar da suka kamu da cutar ta korona:

1. Gwamnan jihar Bauchi:

An gwada gwmanan Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya Bala Muhammed kuma sakamakon ya nuna yana dauke da cutar a wuraren watan Maris na 2020.

Mai magana da yawun gwamnan Muktar Gidado ta cikin wata sanarwa ya ce sai da hukumar NCDC ta gwada gwamnan sau shida tukunna aka tabbatar yana dauke da cutar.

A ranar 9 ga watan Afrilu ne gwamnan ya sanar a Twitter cewa an masa gwaji kuma ya warke daga cutar.

2. Gwamnan jihar Kaduna:

A ranar 29 ga watan Maris, Gwamnan Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai ya sanar da cewa yana dauke da cutar korona.

Ya kuma kara da cewa ya killace kansa kamar yadda NCDC ta ba da shawara, musamman ga mutanen da suka kamu da cutar ba tare da nuna alamu ba.

Sai dai kuma a ranar 23 ga watan Afirilu, El-Rufa'i ya kara sanar da cewa sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna ba shi da cutar, bayan kusan shafe kwanaki 14 yana karbar kulawa ta musamman.

3. Gwamnan Jihar Oyo

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya sanar ta shafinsa na intanet cewa an yi masa gwajin cutar korona kuma ya kamu da ita a ranar 30 ga watan Maris.

Ya kuma ce ba ya nuna alamun kamuwa da cutar amma yana ci gaba da killace kansa.

A ranar 5 ga watan Afirilu gwamnan ya fito ya ce an kara gwada shi ba shi da wannan cuta.

4. Gwamnan jihar Abia:

A ranar 8 ga watan Yuni, sakamakon gwaji ya nuna gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu na dauke da cutar korona.

Bayan haka sai gwamnan ya killace kansa karkashin kulawar wani kwararren likita, wanda ya umarci mataimakinsa ya rike kujerar shugabancin kafin ya koma bakin aiki.

An tattaro cewa har yanzu gwamnan bai warke daga cutar ba.

5. Gwamnan jihar Ondo:

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya zamo gwamna na biyar da ya kamu da cutar a Najeriya. Gwamnan ya sanar da hakan a ranar 30 ga watan Yuni, inda yace bai nuna kowace alama ta cutar ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel