Fitattun 'yan Najeriya 12 da suka rasu a watan Yuni
Da yawa daga cikin mace-macen da aka yi a watan Yuni ya shafi manyan mutane kuma ya matukar girgiza zukatan jama'a.
Wannan watan ya zo da abubuwan ba-zata ga iyalan mamatan masu tarin yawa.
Wadannan mamatan sun tafi har abada amma tarihin da suka kafa ba zai gogu ba har abada.

Asali: UGC
1. Fitaccen mawaki Majek Fashek
Mawakin Najeriya ne kuma marubucin waka. Sunansa Majekodunmi Fasheke amma an fi saninsa da Majek Fashek. Ya rasu a ranar 1 ga watan Yuni yana da shekaru 57 a wani asibiti da ke New York.
An haifesa a Benin City. Mahaifiyarsa 'yar Edo ce yayin da mahaifinsa dan Ijesha ne amma tsatsonsu Benin.
2. Tsohon gwamnan jihar Ondo, Bamidele Olumilua
Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Ondo, Bamidele Olumilua ya rasu a cikin watan Yuni.
Olumilua ya rasu yana da shekaru 80 a duniya a garin Ikere-Ekiti bayan gajeriyar rashin lafiya.
Marigayin tsohon gwamnan ya mulki jihar Ondo daga watan Janairun 1992 zuwa Nuwamban 1993 a jamhuriya ta uku.
3. Alhaji Abubakar Tsav
Tsohon kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Alhaji Abubakar Tsav ya rasu a watan Yuni.
Ya rasu a asibitin tarayya da ke Makurdi kuma an birne shi a garin Makurdi kamar yadda addinin Islama ya tanada.
4. Ibidun Ighodalo
Marigayiya Ibidun Ighodalo matar babban faston Trinity House Church ne, Ituah Ighodalo.
Kyakyawar matar ta aura babban faston a shekaru 13 da suka gabata bayan rabuwarsa da tsohuwar matarsa.
Ibidun mai shekaru 40 ta rasu ta bar mijinta da 'ya'ya biyu.
5. Sanata Bayo Osinowo
Dan majalisar mai wakiltar mazabar Legas ta gabas a majalisar dattawa karkashin inuwar jam'iyyar APC, Sikiru Adebayo Osinowo ya rasu a watan Yuni.
Dan majalisar da aka fi kira da Pepperito ya taba wakiltar majalisar jihar Legas har sau hudu. Ya rasu a sa'o'in farko na ranar wata Litinin.
Ya bar mata daya da 'ya'ya a lokacin da yake da shekaru 65.
6. Farfesa Akinkugbe
Farfesa Oladipo Akinkugbe ya rasu a watan Yunin 2020.
Marigayin yana daga cikin farfesoshin farko na asibitin koyarwa a jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo.
Ya rasu yana da shekaru 86 a duniya.
KU KARANTA: An maka Buratai a kotu saboda kama matar sojan da ya 'zage' shi
7. Ma'aikacin gidan rediyo Dan Foster
Fitaccen ma'aikacin gidan rediyo Dan Foster ya rasu a watan Yuni.
Ya rasu ya bar matar aure daya da 'ya'ya uku.
8. Shugaban kotun daukaka kara ta gargajiya a jihad Kogi
Mai shari'a Ibrahim Shaibu Atadoga ya rasu a watan Yuni.
Ya zama cikakken lauya a 1986 kuma ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.
Atadoga dan asalin karamar hukumar Omala ne na jihar Kogi. Ya yi suna bayan ya rantsar da Kaftin Idris Wada a matsayin gwamnan jihar bayan hukuncin kotun da ya bai wa jihar damar samun gwamnoni biyu.
9. Abiola Ajimobi
Tsohon gwamnan jihar Oyo ne kuma sirikin Gwamna Ganduje na jihar Kano.
An haifa marigayi Ajimobi a ranar 16 ga watan Disamban 1949 ga iyalan Ajimobi da ke Ibadan.
Bayan kammala karatunsa a fannin kasuwancin, ya aura Florence Ajimobi a 1980. Suna da yara biyar. Ya yi shugabancin jihar Oyo har sau biyu.
10. Tsohon dan fim Ogun Majek na Nollywood
Fitaccen dan fina-finan Yarbawa, Gbolagade Akinpelu wanda aka fi sani da Ogun Majek ya rasu a watan Yuni.
Ya rasu a gidansa da ke Ibadan bayan doguwar jinyar da ya sha.
11. Alkalin alkalan jihar Kogi
Mai shari'a Nasir Ajanah ya rasu a cikin watan Yuni.
Kwararren alkalin dan asalin karamar hukumar Okehi ne ta jihar Kogi. Ya rasu yana da shekaru 64 a duniya.
12. Chief Bode Akindele
Bode Akindele fitaccen hamshakin dan kasuwa ne kuma shine shugaban Madandola Groups.
Ya rasu a ranar 29 ga watan Mayu. Ya saba taimakon al'umma don kuwa ya bada tallafin miliyoyin naira don yakar cutar korona a jihar Oyo da gwamnatin tarayya.
Ya rasu yana da shekaru 88 a duniya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng