Shugaba buhari ya tattauna da Yariman Saudiyya ta wayar tarho
Kafar yada labarai ta Press Agency da ke Riyadh ta rawaito cewa Yariman kasar Saudiyya, Muhammad Bin Salman, ya yi hira da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da takwaransa na kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa.
Yayin tattaunawarsu, shugabannin sun yi magana a kan kara kulla zumunci da juna da kuma sauran wasu batutuwa da suka shafi bukatun kasashensu da tallafin da zasu iya bawa juna wajen cimma manufofinsu.
Yarima Salman da Buhari sun kara tattaunawa a kan daidaita farashin man fetur a kasuwar duniya a matsayinsu na shugabannin kasashen da ke zaman mambobi a kungiyar kasashe ma su arzikin man fetur (OPEC).
Kazalika sun kara tattaunawa a kan hanyoyin sake inganta kyakyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng