Babu mamaki wani na’u’in COVID-19 ya bulla a kasar nan - Masana

Babu mamaki wani na’u’in COVID-19 ya bulla a kasar nan - Masana

Wasu shararrun masana harkar kiwon lafiya sun ce a yadda cutar COVID-19 ta ke yaduwa, akwai yiwuwar Najeriya ta samu wani sabon samufuri na Coronavirus.

Shugaban jami’ar Redeemer’s University da ke jihar Osun watau Oyewale Tomori, ya shaidawa jaridar Punch cewa watakila wani irin na’u’i na cutar ya bayyana a Najeriya.

Farfesa Oyewale Tomori wanda masani ne a kan harkokin cututtuka, ya bayyanawa ‘yan jarida cewa idan har cuta ta na yaduwa, ta na kara samun damar hayayyafa, za ta iya fito da wani sabon nau’i.

Idan har cutar ta hayayyafa, za a samu sabon samfuri na Coronavirus wanda zai zama babu inda ake da irinsa a Duniya face Najeriya.

A halin yanzu akwai nau’uka uku na COVID-19 a Najeriya wadanda aka shigo da su cikin kasar daga ketare. Masana su na kasa nau’ukan zuwa A, B.1 da B2-1.

A cewar masanin harkokin cututtukan, wani bincike da cibiyar nazarin cuttuka ta RUN ta yi tare da hukumar NCDC ya nuna cewa SARS-CoV-2 ta shigo Najeriya ne ta jikin wani bature.

KU KARANTA: Masu bincike sun gano wata cuta mai kama da COVID-19

Babu mamaki wani na’u’in COVID-19 ya bulla a kasar nan - Masana
Shugaban hukumar NCDC
Asali: Twitter

“Nazarin da aka kara yi a cibiyar ACEGID ta jami’ar RUN, ya nuna cewa asalin samfura kusan 20 na SARS-CoV-2 da ake da su, sun fito ne daga A, B.1 da B2-1.”

“Samfurin A ya samo asali ne daga kasar Sin – wanda aka shiga da shi zuwa kasashen Kudu maso gabashin Asiya, da Jafan, Koriya ta kudu, Australiya, da kuma Amurka.”

“Nau'in B.1 ya fito ne daga kasar Italiya inda annobar ta barke, yayin da B.2-1 ya samo asali daga Birtaniya, Australiya, Amurka, Indiya, Ghana da wasu kasashen nahiyar Turai.”

“Binciken nan da aka yi ya tabbatar da cewa an shigo da nau’ukan COVID-19 dabam-dabam a Najeriya.”

Tomori ya ke cewa nau'in cutar da ta rikida, ta fara harbin ‘yan Najeriya, har ta yi wa wasu mutane uku mummunan kamu. Hayayyafar cutar ya na jawo ta ci karfin rigakafi inji farfesan.

Kawo yanzu NCDC mai takaita yaduwar cutar COVID-19 ta tabbatar da cewa fiye da mutane 25, 000 su ka kamu da cutar. A jihar Legas ne aka fi fama da wannan cuta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel