An maka Buratai a kotu saboda kama matar sojan da ya 'zage' shi

An maka Buratai a kotu saboda kama matar sojan da ya 'zage' shi

Matar wani soja, Mrs Victoria Idakpini da mijinta, Lance Corporal Martins Idakpani sun yi karar Rundunar Sojin Najeriya, Shugaban hafsin sojojin kasa da Attoney Janar na kasa saboda take hakkin bil adama.

An kama Mrs Idakpani ne a makon da ta gabata kwanaki kadan bayan kama mijinta, Martins Idakpani, saboda cin mutuncin Shugaban rundunar sojojin kasa, Lt Janar Tukur Buratai, da Shugaban hafsoshin tsaro, Gabriel Olonisakin cikin wani bidiyo da ya rika yawo a intanet.

A cikin bidiyon, sojan ya yi kira ga shugabanin sojojin da su yi murabus tunda sun gaza wurin yaki da ta'addanci.

An maka Buratai a kotu saboda kama matar sojan da ya 'zage' shi
An maka Buratai a kotu saboda kama matar sojan da ya 'zage' shi
Asali: UGC

Ya kuma zarge su da nuna halin ko in kula da a kan batun tsaro a kasar da kuma yadda yan taadda ke cin karensu ba babbaka a kasar.

DUBA WANNAN: Bidiyon wani mutum da mace suna lalata a kan titi cikin motar UN ya jawo cece-kuce

Ma'auratan cikin wani takardar kara da wani Apeh Abuchi ya shigar a madadinsu, sun ce an hana su ganin lauya kuma ba a sanar da su laifin da suka aikata ba tun kama su a makon da ta gabata.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Akinyodem wanda shine shugaba na kasa na kungiyar lauyoyi ta Revolutionary Lawyers’ Forum, ya bayyana cigaba da tsare ma'auratan a matsayin saba doka.

Lauyan ya ce cikin sanarwar, "Yanzu muka shigar da kara a Babban Kotun Tarayya a kan Rundunar Sojojin Najeriya, Shugaban sojojin kasa da Attoney Janar na kasa saboda tsare Lance Corporal Martins da matansa Mrs Victoria Idakpini ba bisa ka'ida ba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel