'Yan bindiga sun kashe likita, dansa da abokinsa bayan karbar N7.5m

'Yan bindiga sun kashe likita, dansa da abokinsa bayan karbar N7.5m

Jami'an binciken sirri sun damke wasu yan kungiyar masu garkuwa da mutane da ake zargi da kashe mutum uku bayan sun karbi kudin fansa har N7.5 miliyan daga iyalansu.

Kakakin rundunar 'yan sanda, DCP Frank Mba, ya bayyana hakan a Abuja a ranar Litinin yayin da suka damko wasu mutum 26 da ake zargi da garkuwa da mutane, fashi da makami, mallakar makamai da sauran laifuka.

Kamar yadda ya ce, kungiyar masu garkuwa da mutanen sun sace wani Dr Ausu Benedict, dansa da abokinsa a kan hanyarsu ta zuwa Abuja.

A yayin da suke hannunsu, wadanda ake zargin sun tuntubi iyalansu inda suka karbi N7 miliyan a matsayin kudin fansa.

'Yan bindiga sun kashe likita, dansa da abokinsa bayan karbar N7.5m
'Yan bindiga sun kashe likita, dansa da abokinsa bayan karbar N7.5m Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun tashi gari kacokan a jajiberin zaben kananan hukumomi a Taraba

"Kafin karbar kudin fansar, wadanda ake zargin sun tirsasa Benedict ya rubuta Chek din banki na N500,000 wanda suka je suka cire," dan sandan yace.

Mba ya jajanta yadda kungiyar ta kashe wadanda tayi garkuwar da su bayan karbar kudin fansa.

Ya ce, "Daga cikin wadanda ake zargin, mun damke wata kungiyar da ake zargin ta kware wurin ta'addanci a yankin arewa ta tsakiya.

"Sun karba kudin fansa har N7 miliyan daga iyalan Audu Benedict.

"A yayin da suke hannunsu, sun tirsasa likitan ya rubuta chek na N500,000 wanda hakan ya kai kudin zuwa N7.5 miliyan.

"Bayan karbar kudin fansar, sun halaka likitan, dansa da abokinsa."

Ya kara sa bayyana cewa kungiyar ta yi garkuwa da wata Veronica Aboyi, wacce 'yar uwa ce ga daya daga cikin wadanda ake zargin.

Biyu daga cikinsu sun amsa laifinsu.

'Yan sandan sun samu bindigogi kirar AK 47 6 da sauran miyagun makamai.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ya bai wa rundunar soji umarnin gamawa da 'yan bindiga da ke kashe 'yan jihar. Ya kara da cewa kada a bar dan bindiga ko daya da rai.

Masari ya yi wannan kiran ne yayin da ya kai ziyara ga 'yan gudun hijira a kananan hukumomin Faskari, Kadisau da Dandume na jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel