'Yan sanda sun kama 'yan bindigar da su ka kashe Dakta Audu bayan karbar N7.5m kudin fansa

'Yan sanda sun kama 'yan bindigar da su ka kashe Dakta Audu bayan karbar N7.5m kudin fansa

Jami'an 'yan sandan rundunar IRS (Intelligence Response Team) sun samu nasarar kama wasu tawagar ma su garkuwa da mutane da suka kashe mutane uku bayan karbar miliyan N7.5 a matsayin kudin fansa daga hannun 'yan uwansu.

Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Frank Mba, ne ya sanar da hakan a Abuja yayin bajakolin masu laifi 26 da suka hada da ma su garkuwa da mutane, 'yan fashi da makami da ma su safara mugayen mukamai.

Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin ma su laifin ne a yau, Litinin, a hedikwatarta ta kasa da ke birnin tarayya, Abuja.

A cewar Mba, tawagar ma su garkuwa da mutanen ne suka sace Dakta Audu Benedict, dansa, da kuma abokinsa a kan hanyarsu ta zuwa Abuja daga jihar Benuwe.

Dangi da 'yan uwan Dakta Audu sun hada N7m tare da bawa ma su garkuwa da mutane a matsayin kudin fansarsa tare da sauran mutanen da aka kamasu tare.

"Kafin a kai mu su miliyan N7 da suka nema, ma su garkuwa da mutanen sun tilasta Dakta Audu rubuta mu su takardar fitar da kudi har N500,000 saboda su na bukatar wasu kudi cikin gaggawa," a cewar Mba.

Mba ya kara da cewa amma duk da haka sai da ma su garkuwa da mutanen suka kashe Dakta Audu tare da dansa da abokinsa da aka kamasu tare.

'Yan sanda sun kama 'yan bindigar da su ka kashe Dakta Audu bayan karbar N7.5m kudin fansa
'Yan bindigar da su ka kashe Dakta Audu bayan karbar N7.5m kudin fansa
Asali: Twitter

"Daga cikin ma su garkuwa da mu ka kama akwai wadanda su ka addabi jama'ar yankin arewa ta tsakiya.

"Iyalin Dakta Audu sun biya kudin fansa miliyan N7. Kafin a kai wa ma su garkuwa da mutane kudin, sun tilasta Dakta Audu rubuta takardar fitar da kudi N500,000 daga asusunsa na banki.

DUBA WANNAN: EFCC: Kotu za ta janye belin tsohon Sanata Shehu Sani

"Amma duk da sun karbi jimillar kudin da yawansu ya kai miliyan N7.5, hakan bai hanasu kashe Dakta Audu tare da dansa da abokinsa ba," a cewar kakakin rundunar 'ayn sanda.

Kazalika, ya kara da cewa tawagar ma su garkuwa da mutanen sun sace wata mata mai suna Veronica Aboyi, wacce ke da alaka ta jini da daya daga cikin ma su laifin.

Biyu daga cikin ma su laifin; Gwar Henry da Bello sun amsa laifinsu.

Rundunar 'yan sanda ta ce ta kama bindigu samfurin AK47 guda 6, wasu manyan bindigu guda 3, da sauran wasu mugayen makamai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng