'Yan Najeriya za su san mataki na gaba na sassauta doka a ranar Talata
- Gwamnatin tarayya za ta sanar da kashi na gaba na sassauta dokar hana walwala a fadin kasar nan a gobe Talata
- Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari
- 'Yan kwamitin fadar shugaban kasar sun mika rahotonsu ga shugaban kasa don ya amince
Gwamnatin tarayya za ta sanar da kashi na gaba na sassauta dokar hana walwala a fadin kasar nan a ranar Talata, 30 ga watan Yuni, jaridar The Nation ta ruwaito.
Babban sakataren tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus ta fadar shugaban kasa, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a ranar yau Litinin, 29 ga watan Yuni.
KU KARANTA KUMA: Iran ta bada umarnin damke Trump, ta bukaci taimakon 'yan sandan kasa da kasa

Asali: Twitter
Ya yi jawabin ne bayan mambobin kwamitin PTF sun yi taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa.
Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman a kan yada labarai, Bashir Ahmad, ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter.
KU KARANTA KUMA: Ku tsamo 'yan bindiga tare da karar da su - Masari ga rundunar soji
Kamar yadda ya wallafa: "Yau ce rana ta kashe na dokar kulle kashi na II a fadin kasar nan. 'Yan kwamitin fadar shugaban kasar sun mika hukuncin ga shugaban kasa don ya amince. Mataki na gaba za a sanar da shi a gobe, SGF ya sanar."
A baya dai mun ji cewa gwamnatin tarayya ta amince da bude makarantu a fadin kasar nan. Hakan ya biyo bayan taron da ya wakana tsakanin kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Kamar yadda gwamnatin tarayyar ta bayyana, azuzuwan da za su koma bakin karatun sun hada da: aji shida na dukkan makarantun firamare; daliban aji uku da na aji shida na makarantun sakandaren da ke fadin kasar nan.
Hakazalika, gwamnatin tarayyar ta amince da bude shige da fice tsakanin jihohin kasar nan, amma matukar ba a zarta lokutan doka ba.
Gwamnatin tarayyar ta kara da amincewa da sauka ta tashin jiragen sama a cikin fadin kasar nan kadai.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng