EFCC: Kotu ta fara shirin janye belin tsohon Sanata Shehu Sani
- Kotu ta yi barazanar janye belin da ta bayar da tsohon wakilin jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai, Sanata Shehu Sani
- Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Sanata Sani bisa tuhumarsa da karbar kudi daga hannun dan kasuwa, Alhaji Sani Dauda, da sunan za a bawa Ibrahim Magu cin hanci
Jastis I. E. Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayyana cewa zai janye belin Sanata Shehu Sani Sani matukar ya ki bayyana a gaban kotun yayin zamanta na gaba.
Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta gurfanar da Shehu Sani bisa tuhumarsa da zambar kudi da yawansu ya kai dalar Amurka $25 daga hannun wani dan kasuwa, Alhaji Sani Dauda (ASD), da ke Kaduna.
EFCC ta yi zargin cewa Shehu Sani ya karbi kudin ne daga hannun ASD da sunan cewa zai bawa shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, cin hanci domin a warware matsalar da ASD ke fuskanta a hukumar.
Yayin zaman kotun da aka gudanar ranar Litinin, A. A. Ibrahim (SAN), lauyan da ke kare Shehu Sani ya ce wanda ya ke karewa bai samu damar halartar zaman kotu na yau ba saboda an rufe unguwar da ya ke zaune a Kaduna sakamakon mutuwar makwabcinsa da ya kamu da kwayar cutar korona.
DUBA WANNAN: Kwamitin yaki da annobar korona ya sake komawa gaban Buhari da sabbin bayanai
Lauyan hukumar EFCC, Abba Mohammed, ya nuna rashin amincewarsa da uzurin da lauya Ibrahim ya bayar tare da bayyana cewa ya na da shaidu biyu da suka zo kotun daga unguwar da Shehu Sani ke zaune a Kaduna.
Daga nan ne alkalin kotun ya daga sauraron zaman cigaba da shari'ar zuwa ranakun 6, 7, 8, da 9 na watan Yuli.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng