Iran ta bada umarnin damke Trump, ta bukaci taimakon 'yan sandan kasa da kasa

Iran ta bada umarnin damke Trump, ta bukaci taimakon 'yan sandan kasa da kasa

- Kasar Iran ta bada umurnin kamo shugaban kasar Amurka, Donald Trump inda ta roki 'yan sandan kasa da kasa da su taimaka

- Ta amince da kamo sauran wadanda suke da hannu wurin kisan babban Janar din da aka yi kwanakin baya a Baghdad

- Ana dai zargin Trump da wasu mutum 30 da sa hannu wurin harin ranar 3 ga watan Janairu wanda ya yi ajalin Janar Qassem Soleimani

Kasar Iran ta bada damar damko shugaban kasar Amurka, Donald Trump kuma ta bukaci 'yan sandan kasa da kasa da su taimaka.

Ta amince da damko sauran wadanda suke da hannu wurin kisan babban Janar din da aka yi kwanakin baya a Baghdad.

Mai gabatar da kara a Tehran, Ali Alqasimehr a ranar Litinin ya ce ana zargin Trump da wasu mutum 30 da sa hannu wurin harin ranar 3 ga watan Janairu wanda ya yi ajalin Janar Qassem Soleimani.

Alqasimehr bai bayyana sauran da ake zargi tare da Trump ba amma ya jaddada cewa Iran za ta ci gaba da bibiyar shari'ar koda bayan ya sauka daga shugabancin kasa.

A halin yanzu, 'yan sandan kasa da kasa da ke Lyon, Faransa, ba su yi martani a kan umarnin ba.

Alqasimehr ya ce a sanar da Trump tare da sauran wadanda ke da hannu a harin.

Iran za ta kashe wani dan leken asiri da ke da hannu a kisan Soleimani.

KU KARANTA KUMA: Mutuwar Hama Bachama: Gwamnatin Adamawa ta bada hutun kwanaki uku

Jami'an tsaro a kasar sun damke wani mutum da ake zargin dan leken asiri ne.

Sanarwar da aka bada ba zata iya sa a kama mutum a wasu kasashe ba sai dai za a iya hana shi yawo zuwa wasu kasashen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel