An umarci rundunar 'yan sanda ta biya mambobin kungiyar Shi'a diyyar N15m

An umarci rundunar 'yan sanda ta biya mambobin kungiyar Shi'a diyyar N15m

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta umarci rundunar 'yan sandan Najeriya ta biya diyyar miliyan N15 ga wasu mambobin kungiyar IMN (Islamic Movement of Nigeria), wacce aka fi sani da Shi'a, saboda kisan wasu 'yan uwansu guda uku.

Da ya ke yanke hukunci a ranar Litinin, alkalin kotun, Jastis Taiwo Taiwo, ya umarci babban asibitin kasa da ke birnin tarayya, Abuja, ya gaggauta sakin gawar mambobin da ke ajiye a asibitin bayan an kashesu.

Yayin karanta hukuncin, Taiwo ya ce rundunar 'yan sanda za ta biya diyyar miliyan N5 a kan kowanne ran mutum guda daga cikin mambobin uku da su ka mutu.

Sai dai, alkalin kotun ya ki amincewa da bukatar masu kara na umartar rundunar 'yan sanda ta wallafa sakon bayar da hakuri ga kungiyar IMN a manyan jaridun kasar nan guda biyu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa wadanda mambobin kungiyar IMN ta ambata a cikin takardar shigar da kara a gaban kotun sun hada da babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP) da darektocin babban asibitin kasa da ke Abuja.

Kungiyar IMN ta yi zargin cewa jami'an rundunar 'yan sanda sun kashe mambobinta guda uku da suka hada da Suleiman Shehu, Mahdi Musa, Bilyaminu Abubakar Faska da Askari Hassan yayin gudanar da zanga - zangar lumana a ranar 22 ga watan Yuli, 2019.

An umarci rundunar 'yan sanda ta biya mambobin kungiyar Shi'a diyyar N15m
An umarci rundunar 'yan sanda ta biya mambobin kungiyar Shi'a diyyar N15m
Asali: Facebook

Dandazon mambobin kungiyar IMN sun yi tururuwar fitowa tare da mamaye babbar sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja yayin gudanar da wata zanga - zagar lumana a ranar 22 ga watan Yuli na shekarar 2019 domin neman a saki shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky, tare da matarsa.

DUBA WANNAN: 2023: Kar ku zabi duk dan takarar da aka tsayar a APC ko PDP - Matasan arewa sun bayyana shirinsu na gaba

A cewar kungiyar IMN, an ajiye gawar mambobinta uku; Suleiman Shehu, Mahdi Musa da Bilyaminu Abubakar Faska, a babban asibitin kasa da ke Abuja yayin da su ka yi zargin cewa an ajiye gawar Askari Hassan a reshen asibitin da ke unguwar Asokoro.

Wadanda su ka shigar da kara; Ibrahim Abdullahi, Ahmad Musa, Yusuf Faska da Said Haruna, sun yi ikirarin cewa mambobin IMN da aka kashe 'yan uwa ne garesu.

Har aka kammala sauraron karar, rundunar 'yan sanda ba ta aika wakilci ko tura lauyan da zai kareta a kan zarge - zargen da mambobin na IMN ke yi mata ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel