Covid-19: Buhari zai sanar da mataki na gaba a kan yakar annobar

Covid-19: Buhari zai sanar da mataki na gaba a kan yakar annobar

- Ana sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai amince da mataki na gaba kan yaki da annobar Coronavirus

- Za a yi taro tsakanin shugaban kasar Najeriya da kwamitin yaki da annobar korona na fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 29 ga watan Yuni

- Kwamitin za su sanar da shugaban kasa mataki na gaba da ya kamata a dauka a fadin kasar nan don yakar annobar

A yau ne 'yan Najeriya ke sanya ran cewa gwamnatin tarayya za ta cire dokar hana shige da fice tsakanin jihohin kasar nan idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na'am da mataki na gaba na yakar cutar.

Taron da za a yi tsakanin shugaban kasar da kwamitin za a yi shi ne a ranar Litinin, 29 ga watan Yuni, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ana tsammanin shugaban kasa Buhari zai amince da mataki na uku na yaki da cutar.

Kwamitin zai gabatar da yadda 'yan Najeriya suke bin dokokin dakile yaduwar cutar tare da bada shawarar yadda za a yi a mataki na gaba a kasar nan kan annobar.

Covid-19: Buhari zai sanar da mataki na gaba a kan yakar annobar
Covid-19: Buhari zai sanar da mataki na gaba a kan yakar annobar Hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

A ranar Alhamis, 25 ga watan Yunin 2020, shugaban kwamitin yaki da cutar, Boss Mustapha ya ce za a sanar da 'yan Najeriya mataki na gaba da za a dauka don yaki da cutar bayan taron.

KU KARANTA KUMA: Ku tsamo 'yan bindiga tare da karar da su - Masari ga rundunar soji

Ya ce mataki na biyu shine yadda aka sassauta dokar kullen wanda zai kare nan ba da dadewa ba. Hakan na nufin akwai bukatar saka sabuwar doka.

'Yan Najeriya na ta magana a kan bude walwala tare da bada sassauci a kasar. Sun hada da bude makarantu tare da aminta da shige da fice tsakanin jihohi.

A daya bangaren, hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) ta sanar da karin mutum 490 da aka tabbatar suna dauke da muguwar cutar a Najeriya. A halin yanzu, jimillar masu cutar ya hararo 25,000.

A baya mun ji cewa sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a ranar Alhamis ya ce za a sake kulle Najeriya da yana da karfin ikon aikata hakan.

Mustapha ya ce duk da ba za a so komawa kullen ba, shine abinda yafi cancanta idan aka duba halayyar wasu 'yan Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel