Na daɗe da sanin akwai yaudara tsakanin Tinubu da Buhari - Adebanjo

Na daɗe da sanin akwai yaudara tsakanin Tinubu da Buhari - Adebanjo

A baya bayan masu sharhi na ganin cewa da yiwuwar kyakkyawar alakar da ke tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu, ta yanke.

Wannan lamari ya biyo bayan rikice-rikicen da suka kunno kai dangane da kwamitinin gudanarwa da kuma shugabancin jam'iyyar mai mulki a kasar ta APC.

Sanadiyar hakan ne ya sa jigon kungiyar Yarbawa ta Afenifere, Cif Ayo Adebanjo, ya bayyana cewa daman can ya daɗe da sanin cewa shugaban kasa Buhari yaudarar Tinubu ya ke yi.

Haka zalika Adebanjo ya sanar da cewa, Tinubu kan sa yaudarar shugaban kasar ya ke yi. Ya bayyana jam'iyyar APC a matsayin taron yu-yu-yu da ba bu jituwa a tsakaninsu.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Adebanjo ya bayar da hujjar cewa jam'iyyar APC ba ta dauko akidar da za ta hada kan mambobinta ba, domin dukkaninsu neman kujerar iko suka sa gaba.

Cif Ayo Adebanjo
Hakkin mallakar hoto: Jaridar Tribune
Cif Ayo Adebanjo Hakkin mallakar hoto: Jaridar Tribune
Asali: Facebook

Duk da cewa fadar shugaban kasa ta ce sam babu wata ɓaraka tsakanin Buhari da Tinubu, sai dai hakan ya sha ban-ban da ra'ayin masu sharhi dangane da shawarar da kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC ya yanke.

A ranar Alhamis ne kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC ya rusa kwamitin gudanarwa na jam'iyyar wanda Adams Oshiomhole ke jagoranta tare da nada sabbin masu rikon kwarya.

Wasu na kallon hakan a matsayin wani babban kalubale ga shirin takarar shugaban kasa da Tinubu ke da niyyar yi a 2023 duba da kusancinsa da Oshiomhole.

KARANTA KUMA: Mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun zarta 24, 000 - NCDC

Adebanjo yana cewa, "ina taya Tinubu damuwa, kuma duk ya san yadda sha'anin siyasa ya ke kasancewa, amma ya dage har sai da ya tabbatar Buhari ya zama shugaban kasa."

"Na fadi haka a bainar jama'a cewa Buhari yana yaudarar Asiwaju kuma Asiwaju yana yaudarar Buhari. Kowanensu na ƙoƙarin amfani da ɗayan domin cimma burinsa."

"Ina maganar sauya fasalin kasa wanda ita ce akidar da ta sa Tinubu ya dage a kan sai Buhari ya zama shugaban kasa?"

"Na shafe shekaru 70 a harkar siyasa, da yawan mutanen da ke tsomo baki a yanzu ba a haife su ba lokacin da na fara siyasa, hatta Buhari a lokacin bai gama koyon tafiya ba, du-du-du shekarunsa 74."

"Na dade ina fada, me yasa Tinubu da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da duk wadanda a da suke jam'iyyar AD (Alliance for Democracy) suka koma jam'iyyar APC? Me ya sa suke baya-baya a kan akidarsu ta sauya fasalin kasa?"

"Duk abubuwan da na fada muku yanzu ba shine karo na farko ba. Na sha fadin cewa ya kamata Tinubu da Osinbajo su fice daga jam'iyyar APC. Na fada a bayyane. Abin kunya ne kuma koma baya ne ga kasar Yarbawa."

"Don haka, abin da ke faruwa yanzu a jam'iyyar APC, ya nuna cewa zaman doya da manja kawai ake yi a tsakaninsu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel