Ma’aikatan bogi su na wawurar Miliyan 600 duk wata a Jihar Neja - Kwamiti
An gano wata badakala da ake tafkawa ta inna-naha a jihar Neja, inda aka bankado cewa ma’aikata akalla 11, 000 da ake da su a jihar, na bogi ne wadanda ke cin albashi a bagas.
Wadannan ma’aikata 11, 000 na bogi su na tashi da albashin Naira miliyan 627 duk wata a jihar.
Shugaban hukumar kula da albashi kuma kwamishinan ayyuka da gine-ginen abubuwan more rayuwa na jihar Neja, Injiniya Ibrahim Panti ya bayyana wannan a ranar 28 ga watan Yuli, 2020.
Da ya ke magana a gidan rediyon gwamnati a garin Minna jiya, Ibrahim Panti, ya ce dole a tantance duka ma’aikatan jihar a dalilin makudan kudin da gwamnati ta ke kashewa a sama.
Panti ya bayyana cewa gwamnatin jihar Neja ba za ta iya cigaba da kashe irin wannan kudi ba. Wannan bincike ya sa har yanzu ba a biya ma’aikata albashin watan Yuni ba inji kwamishina.
98% na kason da jihar ta ke samu daga asusun FAAN na gwamnatin tarayya ya na tafiya ne wajen biyan albashi. Wannan ya na nufin 2% kacal ya ke ragewa gwamnati wajen yin wasu ayyukan.
KU KARANTA: Mutane kusan 360, 000 su ke rububin aikin N-Power a kowace sa’a
Kamar yadda kwamishinan ya bayyana, 30% na rukunin ma’aikatan da aka kira domin a tantancesu, ba su bayyana ba, haka kuma akwai ma’aikata masu takardun shaida na bogi.
“Daga cikin ma’aikata 1, 000 da aka gayyata a tantance, 600 zuwa 700 kadai su ka bayyana, inda sauran kuma ba a gansu ba.”
“Kusan ma’aikata 36, 000 aka ce gwamnati ta na da su, amma da kwamitinmu ya fara aiki, mun samu ma’aikata 27, 000, daga baya yawansu ya koma 25, 000.”
“Daga baya mun gano ma’aikata da sunaye daban-dabam amma kuma su na dauke da lambar banki na BVN guda, dauke da albashi da alawus na bogi.” Inji Panti.
Panti ya ce wannan karo, gwamnati za ta hukunta wadanda aka samu da laifi. Kwamishinan ya ce ‘yan kwamitin na sa su na fuskantar barazana, amma duk da haka za su tsaya tsayin daka.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng