Uwargidar marigayi Ajimobi da mataimakin gwamnan jihar Oyo sun yi musayar kalamai (bidiyo)
- Florence Ajimobi, uwargidar marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo Ajimobi, ta yi musayar yawu da mataimakin gwamnan jihar
- Misis Ajimobi ya yi korafin cewa Gwamnatin jihar Oyo bata yi wa iyalan ta’aziyyar mutuwar mijinta ba
- Kokarin bayani da mataimakin gwamnan ya yi ya sa Misis Ajimobi ya mayar da martani cikin dacin rai, inda hakan ya sanya sauran gwamnonin da ke wajen shiga lamarin
Florence Ajimobi, uwargidar marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ta yi musayar yawu da mataimakin gwamnan jihar Oyo, Rauf Olaniyan, kan mutuwar mijinta.
A wani bidiyo da jaridar Nigerian Tribune ta wallafa an nuno mutanen biyu suna musayar kalamai a bainar jama’a a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuni.
Jaridar ta yi bayanin cewa an yi musun ne a lokacin da wasu gwamnoni suka je yi mata ta’aziyya tare da iyalan Ajimobi.
A bidiyon, an gani Misis Ajimobi tana korafin cewa gwamnatin bata yi wa iyalan ta’aziyyar mutuwar mijinta ba.
Kalamanta: “Ina ganin abu mafi karanci da kowa zai iya yi, a matsayin mutum mai tsoron Allah, shine aika kalaman karfafa gwiwa a wannan lokacin. Kuma ko bayan da ya mutu, hatta da kai, mataimakin Gwamna babu wanda ya kira ni...”
Sai mataimakin gwamnan ya katse mata hanzari ta hanyar fadin, “na kira ki.”
Da take mayar masa da martani, uwargidar tsohon gwamnan ta ce: “Da sai ka aika da sakon waya.
KU KARANTA KUMA: Zamfara, Katsina da Sokoto: Dakarun soji sun ragargaza 'yan bindiga
“Bani da lambarka, ba zan iya dauka ba. Ni matar dan siyasa ce, bana daukar lambar da ban sani ba. Kana iya aika sakon waya. Kowa ma zai mutu. Mijina ya mutu, kuma ya yi wa wannan jihar hidima na shekaru takwas. Me muke fadi."
Sauran gwamnonin da ke wajen irin su Abdullahi Ganduje na Kano sun shiga lamarin inda suka bukaci bangarorin biyu su wanzar da zaman lafiya.
A baya mun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta tura jami'anta gidan marigayi tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi.
Gwamnatin jihar bata amince da inda iyalansa suka zaba don binne mamacin ba.
A lamarin lokacin da jaridar The Nation ya ziyarci wurin, ta samu motar 'yan sanda biyu, motar sintiri daya da kuma wata mota kirar Kia Rio wacce jami'an tsaron farin kaya suka ajiye a kusa da wurin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng