Kaduna: 'Yan sintiri sun kashe matashi mai shekaru 17 - 'Yan sanda

Kaduna: 'Yan sintiri sun kashe matashi mai shekaru 17 - 'Yan sanda

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai shekaru 17 a karamar hukumar Zaria yayin da kungiyar 'yan sintirin jihar suka kama shi.

Kungiyar ;yan sintirin ta damke matashin sakamakon zarginsa da take da satar wayar salula.

ASP Mihammad Jalige, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Juma'a.

Jalige ya ce kwamandan kungiyar 'yan sintirin da ka Jan Labule a Kofar Doka ta karamar hukumar Zaria, Alhaji Abubakar da wasu mutum shida sun shiga hannun 'yan sandan karamar hukumar.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewa an mika al'amarin ga hedkwatar rundunar 'yan sandan jihar da ke Kaduna don zurfafa bincike.

Mahaifin yaron mai suna Alhaji Dauda da ke Filin Mallawa a karamar hukumar Zaria, ya sanar da manema labarai yadda lamarin ya faru.

Ya ce dan sa mai suna Muhammad Sani Aliyu ya rasu a hannun 'yan bangar ne yayin da suke tuhumarsa a kan satan wayar salula.

Dauda ya ce, al'amarin ya faru ne a ranar Laraba wurin karfe 2 na rana a Jan Labule da ke Kofar Doka, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya ce wani mahauci mai suna Auwalu, ya zargi dan sa da satar masa wayar salula.

Kaduna: 'Yan sintiri sun kashe matashi mai shekaru 17 - 'Yan sanda
Kaduna: 'Yan sintiri sun kashe matashi mai shekaru 17 - 'Yan sanda. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Katsina: Yadda magidanci ya kashe amaryarsa ya jefa gawarta a rijiya

"A matsayina na mahaifinsa, na tuhumesa amma ya jaddada cewa bashi da masaniya a kan batan wayar.

"Daga baya na bukaci abokina Abubakar Dan-Bakano da ya tuhumesa amma har a lokacin ya shaida wa abokin nawa cewa bashi da masaniya akan batan wayar.

"A yayin da Dan-Bakano ke tuhumarsa, Auwalu ya bayyana tare da 'yan banga wadanda suka daukesa zuwa ofishinsu da ke Jan Labule a Kofar Doka Zaria. A nan ne ya rasa ransa yayin da ake tuhumarsa," ya zarga.

Dauda ya ce 'yan bangar sun yasar da gawar dansa a kasa har zuwa lokacin da ya isa ofishin tare da 'yan sanda.

Kamar yadda yace, 'yan sandan sun dauka dansa zuwa asibitin koyarwa na Ahmadu Bello da ke Zaria inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Mahaifiyar matashi Muhammad Sani, Hannatu Muhammad, ta ce a binciko tare da hukunta wadanda ke da hannu a kisan dan ta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel