Tattalin arzikin Najeriya zai yi mummunan tabarbarewa – Bankin Duniya

Tattalin arzikin Najeriya zai yi mummunan tabarbarewa – Bankin Duniya

- Tattalin arzikin Najeriya ya na fuskantar barazanar da ba a taba gani ba tun a 1985

- Annobar Coronavirus da karyewar darajar danyen mai sun jefa Najeriya a matsala

- Bankin Duniya ya ce a karshen 2020 za a samu karin Talakawa da mutum miliyan 7

Bankin Duniya ya ce annobar cutar COVID-19 da kuma karyewar farashin mai a kasuwar Duniya ya jawo tattalin arzikin Najeriya zai shiga cikin matsalar da aka dade ba a ga irinta ba.

Nazarin da babban Duniya ya yi ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya zai shiga irin halin da ya samu kansa a tsakiyar shekarun 1980. A wancan lokaci soji ne su ke rike da mulki a kasar.

A wani jawabi da babban bankin ya fitar mai taken: “Najeriya a lokacin annobar COVID-19: Shirya tubulin babbako da tattalin arziki’, an yi hasashen tattalin Najeriya zai tsuke da – 3.2% a 2020.

IMF mai bada lamuni a Duniya ta na ganin tattalin kasar zai motsa ne da maki – 5.4% saboda annobar COVID-19. An yi wannan hasashe na a kan kasar za ta ci karfin COVID-19 a karshen bana.

Kamar yadda Hukumar da kuma bankin Duniya su ka nuna, Najeriya ta na samun fiye da 80% na kudin kasar waje ne daga arzikin mai, wanda shi ne 50% na kudin shigan da kasar ta ke samu.

KU KARANTA: Zargin sata: Ibrahim Magu ya maidawa Ministan shari'a martani

Tattalin arzikin Najeriya zai yi mummunan tabarbarewa – Bankin Duniya
Ministar kudin Najeriya, Zainab Ahmed Hoto: NSE
Asali: UGC

Rahoton ya ce: “Da saukar farashin mai a kasuwa, ana sa rai a samu raguwar kudin shiga a asusun gwamnati bayan saukar da karfin GDP zai yi daga 8% zuwa 5% a 2020.”

“Najeriya ta na bukatar tsare-tsare da manufofin tattali da za su zaburar da arzikin kasar.”

Barazanar da kasar za ta shiga zai zarce matsalar kudi kawai, COVID-19 za ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da-dama, kuma annobar za ta jefa mutane miliyan bakwai ko fiye da haka cikin talauci.

Rahoton bankin Duniyan ya ce: “A yayin da ake tunanin cewa talakawa za su karu ne miliyan biyu, saboda karin adadin jama’a, yanzu alkaluman za su tashi ne zuwa mutum miliyan bakwai.”

"Kason marasa hali zai tashi daga 40.1% da aka samu a 2019 zuwa 42.5% a shekarar nan."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel