PDP ta na makokin Abiola Ajimobi, ta ce Najeriya gaba daya ta yi rashi

PDP ta na makokin Abiola Ajimobi, ta ce Najeriya gaba daya ta yi rashi

- Jam’iyyar PDP ta yi magana bayan samun labarin cikawar Abiola Ajimobi jiya

- Tsohon Gwamnan Oyo Abiola Ajimobi ya dade ya na fama da cutar COVID-19

- PDP ta ce mutuwar irinsu Sanata Abiola Ajimobi rashi ne ga daukacin Najeriya

A ranar Alhamis, shugabannin jam’iyyar hamayya ta PDP, sun nuna takaicinsu a game da rasuwar tsohon gwamnan jihar Oyo, kuma tsohon shugaban APC na kasa, Sanata Abiola Ajimobi.

Jam’iyyar adawar ta ce mutuwar ‘dan siyasar ba jam’iyyar APC da jihar Oyo kurum ta shafa ba, Najeriya ce gaba daya ta yi rashi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Sanata Abiola Ajimobi mai shekara 70 a Duniya ya rasu ne bayan ya yi ta fama da cutar COVID-19 na kusan makonni uku a wani asibiti da ke garin Legas.

A wani jawabi da jam’iyyar PDP ta fitar ta bakin mai magana da yawunta, Kola Ologbondiyan, ta ce: “Labarin wannan mutuwa kwatsam ya girgiza mu, musamman a irin wannan lokaci.”

KU KARANTA: COVID-19: Ministan ilmi ya yi magana a kan bude makarantu

PDP ta na makokin Abiola Ajimobi, ta ce Najeriya gaba daya ta yi rashi
Sanata Abiola Ajimobi
Asali: UGC

Kola Ologbondiyan ya ke cewa: “A yanzu ne Najeriya ta ke bukatar mutum mai tarin kwarewa da sanin aiki da dattaku irin Marigayi Ajimobi.”

“Sanata Ajimobi ya kasance kwararren shugaba, jajirataccen ‘dan majalisa, mutum mai neman zaman lafiya, wanda ya bada gudumuwa wajen kawo zaman lafiya da cigaban siyasa da kasarmu Najeriya.”

Kakakin babbar jam’iyyar hamayyar ya kara da cewa: “Jam’iyyarmu ta na hakikanin yi wa Iyalin Ajimobi ta’aziyya, musamman bazawarar da ya bari, Misis Florence Ajimobi da shugaban kasa Muhammadu Buhari, da shugabannin APC na kasa, da gwamnati da mutanen jihar Oyo.”

“Jam’iyyar ta na rokon Ubangiji ya ba Najeriya damar hakurin wannan rashi, tare da jin kan mamacin.”

Dazu nan mu ka ji cewa Shugaban EFCC Ibrahim Magu ya maidawa Ministan shari’a martani a kan zargin da ya jefe sa da su, ya ce babu barazanar da za ta taka masa burki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel